✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tufka Da Warwara: Labari na biyu a gasar Aminiya-Trust

Dambarwar siyasa da makircin gwamna don hana mataimakinsa tsayawa takara.

A rude Gwamna Audu Maikaji ya juyo, ya kalli Babangida Soja, shugaban jam’iyyarsu ta BSC, cikin tashin hankali yake fadin; “Kana so ka ce kashi 75 na deliget dinmu Nuhu agaji za su yi?”

Ya gyada kai ya ce; “Kwarai kuwa! Na samu labarin hakan, musamman ’yan kasuwanninmu da suke ta shige da ficen ganin ya samu takarar nan.”

Gwamna Maikaji ya hasala cikin tsananin damuwa kamar mai shirin fasa ihu ya ce; “Ko kadan ba na fatar Nuhu Agaji ya gaji kujerata.

“Saboda shi wani irin mutum ne da ba a gane gabansa balle bayansa. Amma na fuskanci so ake a yi min bore matukar na ki tsayar da mataimakina.”

Ya yi taku daya zuwa biyu yana muzurai, ya juyo ya fuskanci Babangida ya ci gaba da cewa, “Ka fi kowa sanin Bala Biza shi nake so ya gaje ni. Saboda shi ne zai iya rike mana jihar nan yadda muke so bayan mun bar gwamnati, amma wannan sokon mataimakin nawa yana neman karya min tsari.”

Babangida ya ce; “Ya kamata a san matakin bi dai, domin yanzu haka ’yan jarida da sauran al’umma suna can suna jira domin labari ya karade cewa Gwamna ya shiga ganawar gaggawa da shugaban jam’iyya kasa da awa daya kafin a shiga zaben fid da gwani.”

Gwamna Maikaji ya yi murmushin keta, yana zagaye falon ya juyo ya kalli Babangida ya ce; “Da alama kai ne za ka zama sabon gwamnan jihar nan matukar za ka ba mu hadin kai.”

Cike da mamaki Babangida ya kalli Gwamna Maikaji ya ce; “Your Edcellency, ni kuma, amma ta yaya?”

“Idan har za ka amince da bukatunmu, to shakka babu in Allah Ya yarda kai ne sabon gwamna.” Gwamna Maikaji ya yi furucin, yana murmushi gami da kafe shi da ido.

Cikin sanyin jiki Babangida ya ce; “Da zan samu wannan damar da na yi matukar farin ciki kuma na yi biyayya wajen cika maka muradunka.

“Na yi gwagwarmaya sosai a siyasar jihar nan a matsayina na tsohon kwamishina karo biyu, kuma tsohon dan majalisa, sa’annan tsohon Shugaban Ma’aikatan Gidan Gwamnati, da kuma matsayina na shugaban jam’iyya a yanzu.”

Gwamna Maikaji ya yi murmushi ya ce; “Saura minti nawa a shiga zaben fidda gwanin?”

“Saura minti ashirin da biyar.” Babangida ya ba shi amsa cikin girmamawa.

Gwamna ya jinjina kai ya ce; “A je, a gabatar da zaben, kuma a ayyana Nuhu Agaji a matsayin wanda ya lashe zaben, zan fita yanzu na yi hira da ’yan jarida tare da bayyana wa duniya ina goyon bayan mataimakina.

“Ina so jibi ka fito ka yi hira da ’yan jarida ka shaida wa duniya cewa ka fita daga jam’iyyar BSC saboda rashin adalci da aka yi muku, aka tursasa ku wajen tabbatar da Nuhu Agaji a matsayin dan takara bayan shi ya zo na uku.

“Sannan ka sanar da komarwa ka jam’iyyar PHD, a kan kai ma za ka je neman kujerar gwamna.”

Ya dafa kafadarsa ya ci gaba da fadin; “Na san za ka samu takara a can kuma kana da jama’a sosai, abin da jam’iyyar ke nema a yanzu ke nan.

“Ka yi kokarin daukar mataimaki wanda zai yi mana saukin saukewa idan an yi nasara, za mu bi duk hanyar da ya kamata wajen ganin ka tsige shi domin nada Bala Biza a matsayin mataimaki, wanda hakan zai zama ladar aikin da zai mana a wannan zaben domin shi za mu nada shugaban jam’iyyarmu na riko, na bar ka lafiya gwamna mai jiran gado.”

Yana gama fadin hakan ya juya ya bar falon. Cike da mamaki shi ma Babangida ya bar falon yana ta faman tufka da warwarar zancen.

Yadda suka tsara haka ta tabbata, inda aka ayyana Nuhu Agaji a matsayin wanda ya yi nasara, sannan kuma Babangida ya fito ya shelanta ficewarsa daga jam’iyar BSC tare da sanar da komawa jam’iyyar PHD, inda aka nada Bala Biza shugaban jam’iyya na riko na jam’iyyar BSC ya maye gurbin Babangida.

Duk wani shige da fice da ake yi gwamna Maikaji ne ya yi, inda da kansa ya kaddamar da kwamitin yakin neman zaben Nuhu Agaji, ya kuma fitar da zunzurutun kudi domin kamfen.

Jam’iyyar PHD ta yi matukar farin ciki da zuwan Babangida Soja inda ba wani bata lokaci suka ba shi tikitin takara ba tare da an yi zaben fidda gwani ba.

Da kansu kuma suka ba shi damar zaben mataimaki bayan sun kawo masa sunaye a rubuce.

Bai zaba ba sai da ya tura wa Gwamna Maikaji wanda da kanshi ya zabi wanda yake ganin zai yi musu saukin saukewa.

Makudan kudi Gwamna Maikaji ya ware karkashin shugaban jam’iyya Bala Biza tare da sauran takwarorinsa na kananan hukumomi goma sha hudu da mazabun da suke jihar a cikin wani shiri na yi wa jam’iyya da dan takara zagon kasa.

Cikin daren wata Alhamis Gwamna Maikaji ya yi ganawar sirri da dan takarar gwamna na jam’iyyar adawa ta MSC, wato Dallami Baba, a gidansa da ke Birnin Tarayya inda ya ba shi tabbacin jam’iyyarsu ta shirya mara masa baya domin ganin ya kayar da dan takararta tare da nuna masa ya fi dan takararsu kuma mataimakinsa nagarta da cancantar zama gwamna.

Dallami Baba ya gamsu da bayanan Gwamna Maikaji inda suka yi a rubuce ga mukaman da za a yi wa tsagin Gwamna Maikaji bayan an ci zabe.

Naira biliyan daya ya ba shi gudummawa tare da ba shi tabbacin nan da kwana biyu zai turo wasu jiga-jigan jam’iyyar zuwa tafiyar Dallami Baba.

Kowane dan takara da jam’iyyarsa sun yi kokarin zagaye kananan hukumomi neman kuri’ar talakawa.

A ranar zabe jam’iyyu shida ne suka shiga aka fafata zaben da su a jihar ta Bandawa.

Bayan an gama kada kuri’a, kowane akwati idan aka lissafa kuri’u, wata Babangida Soja na kan gaba, wata kuma Dallami Baba ne ke kan gaba, inda Nuhu Agaji ke take musu baya.

Sai dai an samu hatsaniya a wasu akwatunan da mazabu inda tun a matakin mazabun aka fara soke wasu akwatuna, wadanda a karshe jam’iyya da wakilan ’yan takara suka hallara a babban dakin tattara sakamakon zaben gwamna na jiha domin karbar sakamako.

An gabatar da sakamakon kowace karamar hukuma tare da shaidu bisa ka’ida, inda a karshe bayan tattara sakamako baturen zabe ya ayyana Dallami Baba na jam’iyyar MSC a matsayin wanda ya yi nasarar kayar da Babangida Soja da kuri’u talatin da biyar, sai Nuhu Agaji da ya zo a mataki na uku.

Wakilan jam’iyyu sun karbi sakamako sai dai rashin gamsuwar da tsagin Babangida Soja da suka nuna, inda take Gwamna Maikaji ya dauki lauyoyin da za su mara wa Babangida Soja baya suka shigar da kara.

Su ma tsagin Dallami Baba sun karbi sammaci, sun kuma dauki nasu lauyoyin, sannan ba su fasa shirye-shiryen shiga gidan gwamnati ba.

Zama uku kotu ta yi, ta bayar da umarnin sake zaben wasu akwatuna cikin kwana sha hudu, sai dai Dallami Baba da jam’iyyarsa suka daukaka kara kan hukuncin bai musu dadi ba, inda waccan kotun ta yi watsi da hukuncin kotun farko, Babangida Soja da tawagarsa sun bibiyi shari’ar har zuwa Kotun Koli inda suka yi nasara a nan bayan kotun ta tabbatar da hukuncin kotun farko.

Hakan ba karamin dadi ya yi wa bangaren Babangida Soja da kuma Gwamna Maikaji ba.

Akwatin da za a sake zaben Dallami Baba kuri’a tamanin da shida yake nema ya yi nasara, inda Babangida Soja ke neman dari da sha hudu.

Shiri na musamman Gwamna Maikaji ya yi wa zaben, wanda ana cikin haka ya umarci Bala Biza da ya sanar da barin jam’iyyarsu ya koma ta Babangida Soja tare da mara masa baya.

A ranar zaben, an fafata zaben da duk wata hanya da Dallami Baba ya bi domin ganin ya yi nasara ta gagara, inda Babangida Soja ya yi nasara da kaso uku cikin hudu na kuri’un da suke akwatin.

Cikin kankanen lokaci aka shirya bikin rantsar da sabon gwamna tare da raka shi zuwa gidan gwamnati.

Duk wasu burace-burace na Gwamna Maikaji sun cika inda cikin makon farko ya yi lis na wadanda yake so a nada mukaman kwamishinoni da masu ba da shawara da Sakataren Gidan Gwamnati da kuma Shugaban Ma’aikatan Gidan Gwamnati.

Sai dai fa nan Babangida Soja ya daka tsalle ya dire kan ba zai bi son rai ya yi kitso da kwarkwata ba a gwamnatinsa, sai ya tantance.

Lokacin da sakon ya iske Gwamna Maikaji bai yarda ba, sai da ya tako har ofishin gwamna domin jin gaskiyar hakan, inda Babangida Soja ya ba shi uzurin ba zai samu ganin shi ba yanzu sai wani lokacin in kuma a kan wannan maganar ce to ba fa zai canja ba.

Kasa kyakkyawan motsi ya yi lokacin da sakon ya iske shi, cikin fushin da bai taba riskar kansa a ciki ba, ya kira wayar Babangida Soja, yana dagawa bai jira abin da zai ce ba ya ce, “Da jikina da kudina da lokacina na yi amfani na dora ka a kujerar nan, ina so ka shirya sauka nan da dan kankanen lokaci, yadda na dora ka bai min wahala ba, sauke ka ma ba zai min wahala ba.”

Yana gama fadin hakan ya mike yana fadin; “Wasa farin girki.”