Ƙungiyar Manoma ta Nijeriya reshen Jihar Katsina (AFAN) ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta taimaka musu wajen shawo kan tsutsotsi da ke lalata amfanin gonakinsu.
Shugaban Ƙungiyar AFAN na Kastina, Alhaji Ya’u Umar-Gojo-gojo ne ya yi wannan kiran a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ranar Laraba a Katsina.
- ’Yan sanda sun kama masu ƙwacen waya 985 a Kaduna
- Mun kashe masu tayar da ƙayar baya 2,245 a cikin watanni 3 – Sojoji
Ya ce roƙon ya zama dole domin a duk lokacin da tsutsotsin suka mamaye gonaki, sai su cinye jikin shukar wanda hakan ke sa amfanin gonakin lalacewa.
Umar-Gojo-gojo ya ce matsalar ta yi yawa a wurare musamman kananan hukumomin Batarawa da Mani da Daura da Funtua.
Ya ce, tsutsotsin sun fi cin sabbin amfanin gonar da aka shuka kamar masara da dawa da gero.
Shugaban ya shawarci manoman da wannan matsala ta shafa da su riƙa amfani da maganin kashe ƙwari da aka ba su domin kashewa da hana tsutsotsin yaɗuwa zuwa wasu wurare.
“Mun samu koke-koke daga wasu mambobinmu cewa tsutsotsi na lalata amfanin gonakinsu sosai.
“Mun ziyarci waɗannan wuraren da abin ya shafa kuma mun ga yadda tsutsotsin ke yin ɓarna a gonakin, amma mun shawarce su da su yi amfani da sinadarai da aka ba da shawara wajen kashe tsutsotsin kafin gwamnati ta sa baki don rage asara.”