Barkanmu da warhaka Manyan gobe, tare da fatan alheri kuma kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku labarin ‘tsuntsaye biyu’ labarin ya kunshi yadda kyautatawa ke da ranarta. A sha karatu lafiya.
Taku; Gwaggo Amina Abdullahi
Akwai wasu tsuntsaye mata da miji a wani daji, sun shaku da juna. Rannan sai mijin ya ce bari ya fita don neman masu abin da za su ci. Tun safe da ya fita bai dawo ba har yamma. Sai matar tsuntsun ta shiga damuwa. Ta ce wa kanta mijinta bai taba dadewa haka ba ko lafiya? Tana cikin wannan tunani ne sai ta hangi mijinta a hannun wani maharbi a keji an kama shi, ga hadari ya hadu.
Matar tsuntsu ta yi iya kokarinta domin janye hankalin maharbin ko zai jefar da kejin amma ba ta ci nasara ba. Kawai sai ta ce da shi “barka da zuwa bari na hura maka wuta domin na ga ka jike bayan ruwan saman da aka yi”. Nan da nan ta hada wuta sannan ta ce da maharbin “ bari na gasa maka kaina domin na ga kana jin yunwa.
Tana kokarin fadawa wutar kenan sai maharbin ya tausaya ya ce da ita ta bari, sai ya kwance mata miji a kejin. Daga nan suka yi ta yi masa godiya kafin su koma saman bishiya.