Wasu mutum biyu da jami’an rundunar ’yan sanda ta kai agajin gaggawa (RRS) ta cafke ranar Juma’a bisa zargin aikata fashi da makami sun ce sun yanke sharawar tsunduma sana’ar ne saboda fargabar shiga halin ni-’ya-su in aka sake sanya dokar kulle.
An dai kama mutanen da ake zargin – Rasak Babatunde mai kimanin shekaru 22 da Idowu Wasiu mai kimanin shekaru 16 ranar Juma’a a yankin Otedola dake kan babbar hanyar Legas zuwa Ibadan.
Mutanen, wadanda ’yan sanda suka kuma yi zargin mambobin kungiyar asiri ta Awawa ne da ke Agege, an cafke su ne lokacin da suke tsaka da fashi a kan hanya.
Sai dai wadanda ake zargin sun ce, “Mu mambobin kungiyar asiri ta Awawa ne. Mun daina fashi ne tun da mu ka shiga kungiyar kimanin shekaru hudu da suka gabata saboda tana ba mu abinci da abin sha da kuma mata.
“Mun yanke shawarar komawa fashi ne saboda wahalar da mu ka sha a lokacin dokar kulle ta farko. Ba mu da kudi, ba abinci. Saboda haka ne muka yanke shawarar yin fashin domin mu tara makuden kudade kafin gwamnati ta sake kulle gari,” inji Rasak.
Kakakin Rundunar ’Yan Sanda ta jihar Legas, Muyiwa Adejobi ya ce mutanen biyu ’yan kungiyar asiri ta Awawa ne a yankin Oko-Koto, a Agege, bayan ’yan sanda sun wargaza shirin su na yin fashi a gadar Otedola dake kan hanyar Legas zuwa Ibadan.
“Kwamishinan ’yan sanda na jihar Legas, CP Hakeem Odumosu ya ba da umarnin mamaye dukkan maboyar bata-gari a jihar musamman yankin Agege da kewaye a yunkurin da mu ke yi na rage yawan aikata laifuka a jihar,” inji kakakin ’yan sandan.