Iyayen ’yan matan 317 da aka yi garkuwa da su daga Makarantar Jangebe na fargabar ana iya yi ya ’ya’yan nasu fyade ko su kamu da cututtuka masu hadari a hannun ’yan bindigar.
Wata uwa da ’ya’yanta biyu ke cikin daliban da aka yi garkuwa da su, Safiya Kewaye ta nuna damuwarta kan yiwuwar azabtar da ’ya’yan nasu da yunwa da matsanancin sanyi, da nauo’in cin zarafi da zai dade yana damun su.
- Shafin Aminiya ya dawo
- Salihu Tanko Yakasai yana hannu —DSS
- Yadda gwamnati ta sa muka shiga yin garkuwa da mutane —Auwal Daudawa
“Muna ganin saboda yawan daliban dole yaran su shiga matsananciyar damuwa.
“Masu garkuwar ba za su iya ciyar da yaran masu wannan yawa ba. Ina ma za su samu abincin?
“Muna kuma tsoron za a iya wa ’yan matan fyade, saboda an far musu ne a lokacin da suke barci.
“Wasunsu tsabar tsoro sun kasa daukar zaninsu ko mayafi,” inji matar.
Malam Ibrahim, wanda shi ma aka yi garkuwa ’yarsa ya ce rashin lafiyar yarinyar wadda ke kan karbar magani na iya tabarbarewa a hannun ’yan bindigar.
“Daf da komawarta makaranta mun kai ta asibiti aka duba ta aka ba ta magani. Ta yaya za ta murmure alhali babu abinci ga kuma sanyi?”
“Mun ga yadda Daliban Kankara suka neme bayan da aka sako su saboda tsabar yunwa. Abun zai yi musu wuyan jurewa,” inji shi.
Kwamishinan ’Yan Sandan Zamfara, Abutu Yaro ya ce tuni manyan jami’an Rundunar suka dukufa aikin ceto daliban daga yankin da ake kyautata zaton an boye su.
Ya ce ana aikin ne tare da taimakon helikwaftoci biyu na ’yan sanda baya ga jami’an da suka bazama a doron kasa.
Kakakin Rundunar, SP Muhammad Shehu, told ya bukaci jama’a su kwantar da hankali, yana mai cewa ’yan sanda na da duk abin da ake bukata domin ceto ’yan matan.