✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Tsoron Allah ne ginshikin samun nasara a shugabanci’

Tsohon Shugaban Direbobin kananan Motoci masu Cin Dogon Zango na kungiyar NURTW ya ce shugabancin yana bukatar wasu abubuwa domin tafiyar da shi kamar yadda…

Tsohon Shugaban Direbobin kananan Motoci masu Cin Dogon Zango na kungiyar NURTW ya ce shugabancin yana bukatar wasu abubuwa domin tafiyar da shi kamar yadda ya dace.
Alhaji Nasiru ya ce abubuwan sun hada da hakuri da ilimi da sauransu.
Ya ce, “kasancewa nayi shugabancin wannan kungiya na wani tsawon lokaci ya sa na fahimci abubuwa da dama a kan shugabanci musamman na kungiya wadda ma fi yawa aka fi sani da cewa ayyukan sa-kai sun fi yawa.”
Ya ce bayan tarin matsalolin da shugancin ya ke da shi, “saboda idan aka lura bambancinsa da na gwamnati shi ne biyan albashi, amma duk wata kwaramniya iri daya ce.
Za ka shugabanci mai hankali da maras shi, mai hali da akasin haka, dan gida da bako kuma kowa ya taso sai ya ce, ina shugaba?,” inji shi.
Ya ci gaba da cewa “duk wanda zai yi jagoranci kungiya koma wane iri ne, sai ya tana ji wadannan abubuwa hudu da na ambata.”
Kamar yadda tsohon shugaban kungiyar ya ce, “hakuri shi ne babban abu da mai shugabanci zai fara rikewa bayan ya sanya tsoron Allah a ransa.”