Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jinkai. Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah, Ubangijin halittu. Tsira da amincin Allah su tabbata ga mafificin halittu, Annabi Muhammadu dan Abdullahi, tare da alayensa da sahabbansa da duk wanda ya shiryu da shiriyarsa, ya siffatu da sunnarsa, har zuwa Ranar Sakamako.
Bayan haka, muna nan dai a kan hanyarmu ta zuwa Aljanna. Muna tare da kudurce-kudurcenmu guda uku, yau za mu ci gaba ne daga:
4. Mu kudurce, muna masu tabbatarwa cewa bukatar da al’umma take da ita ga Annabawa da Manzanni (da Manzon Allah (SAW) shi ne na karshensu), wadanda za su nuna musu hanyar zuwa Aljanna, shi ne dalilin aiko su. Dalilin da ya sa aka aiko Annabawa, shi ne don su nuna wa al’umma hanyar da za a bi don komawa cikin wancan gida da Shaidan ya fito da babanmu (Annabi Adam AS) daga cikinsa. Wannan ita ce hikimar aiko Manzanni.
Ashe ke nan, idan mutum ya ki bin Manzo, to ya gama yawo ya tabe, ya yi asara! Saboda haka aka saukar da littattafai gare su (Manzannin)! Daga nan ne, ka ga ya zama dole a gaskata daukacin Manzanni (AS) (wadanda a wasu wurare an nuna su dubu dari da ashirin da hudu – 124, 000 ne; sannan aka ware, a cikinsu akwai kimanin dari uku da goma sha hudu – 314, wadanda Mazanni ne da a cikinsu aka ware guda ashirin da biyar – 25, wadanda su kuma daga cikinsu guda biyar – 5 su ne Ulul Azmi (wadanda suka fi daukaka ko daraja). Ashirin da biyar – 25 din nan, wajibi ne kowane Musulmi ya san su. Biyar – 5 din kuma, a kebance lallai ne a san su, a san littattafan da aka ba su, a san tarihinsu, wanda in ba a san tarihin ba, akwai matsala dangane da haka). Lallai mu yi imani da su a dunkule, a duk inda aka dunkule su, inda ka ware su kuma aka fade su daki-daki su ma a san su. Haka nan da yin da’a (biyayya) gare su da wajabcin yin imani da littattafan da aka ba su tare da aiki da abin da ke ciki na abin da Allah bai soke ba. Don akwai hukunce-hukuncen da aka canja a kan al’ummar farko zuwa ga al’ummar Manzon Allah, (Sallallahu Alaihi Wasallam) da waninsu na dokoki da hukunce-hukunce.
5. Haka dai abin yake, kamar yadda dole kuma sai an yi imani da mala’iku. Imani da mala’ikun nan ba kawai a ce an yarda, an amince ba ne. Mala’ikun nan Allah kadai Ya san iyakar yawansu – farko a yarda a haka din, suna nan da yawa. Sannan wadanda ya ware daga cikinsu – wato mukarrabuna (makusanta) guda goma – 10 a san su, a san sunayensu, a san ayyukan da suke yi, domin kowanensu da abin ya kebanta da shi. A san Mahaliccinsu (Mala’ikun nan) Ya halitta su daga haske, su ba mata ba ne, ba maza ba ne, ba su ci, ba su sha, ba su barci, ba su gajiya, ba su auratayya, sannan ba su saba wa Allah kan abin da Ya umurce su, suna aikata abin Allah Ta’ala Ya sa su, masu karfi ne… lallai ne a san wadannan siffofi nasu! Malamai duk sun yi wadannan bayanai. Shi ne ake bukatar mutum ya san wannan, ya san mala’iku, ya yi imani da su!
6. Haka nan a yi imani da kaddara da makoma. Mutum ya yarda akwai kaddara ta alheri ko ta sharri! Sannan ya yarda bayan an gama wannan zama na duniyar nan, za a mutu, za a koma cikin kabari a yi rayuwar barzahu (wuri ne tsakanin duniya da Lahira), zama ne na iyakar yadda Allah Ya so, sannan a tashi a je makoma gaba daya, inda za a saka wa kowa da aikin da ya kasance yana aikatawa – ko a tafi Aljanna (Allah Ya ba mu dacewa da samunta), ko a tafi Wuta (Allah Ya kiyashe mu Ya nisantar da mu daga gare ta). Wannan shi ne mutum ya yarda da hisabi da sakamakonsa. Ba Musulunci ba ne mutum ya ji cewa in an mutu shi ke nan!
Da wadannan jerin abubuwa guda shida, idan aka dube su, aka lura da su, za a ga al’amura ne da suka tattaro imani ingantacce. Idan muka tsare wadannan abubuwa, to yanzu mun ci rubu’in (kashi daya cikin hudu na) tafiyarmu zuwa Aljanna!
Kashi na biyu na tafiyar:
Yanzu ya ku ’yan uwa abokan tafiya zuwa Aljanna, ku taso mu tunkari rubu’i na biyu na wannan tafiya, wanda shi ne ya kunshi ayyuka na kwarai. Ku taso gaba daya, ku jajirce, kada ku yi sanya, kada wani ya ce ya gaji, zai fita. Tunda dai imani ya samu, to kuma ai sai aiki na kwarai ya bi bayansa:
1. Farko a wannan tsarin shi ne tsayar da Sallah. Mu kasance mun san yadda za mu yi tsarki cikakke. Da yawa mutane tun daga tsarkin nan suke barin sallarsu. Dole ne mutum ya tsaya, kada ya yi girman kai, ya tambaya; bacewar hanyar (shiriya) ita ce asara, amma in an kama nemanta, to ba a makara ba. Kawai ka koma ka tambaya yaya ake tsarki? Yaya za a gane yanayin ruwan da za a yi tsarkin da shi? Duk shari’a ta nuna mana yadda za a yi, ba ta bar komai ba, sai da ta rarrabe shi dalla-dalla. Saboda haka, dole a koma a kalli yadda za a yi tsarki cikakke.
Sannan mu yi sallar a daidai lokacin da aka ce a yi, kada mutum ya bari sai sa’ar da ya ga dama. Kuma ta kasance a cikin jama’a (cikin jam’i) – kada mutum ya rika zuwa can su yi wata ’yar majalisa, ga masallaci a kusa da su su rika cin abinci a wurinsu daban, su ki zuwa masallaci – in an yi musu magana su ce, ‘Ko’ina ne.’ Ba daidai ba ne su yi haka!
Mu yi sallar nan cikakkiya, muna cika dukkan sharuddanta (ka ga dole dai sai an koma an nemi ilimin fikihu – inda a nan ne za a gane wadannan hukunce-hukunce) da farillanta da sunnoninta da ladubban da ke ciki. Ta yin haka, sai mu dace da irin sallar Manzon Allah, (Sallallahu Alaihi Wasallam), saboda ya ce, “Ku yi Sallah kamar yadda kuka ga ina Sallah.” To da sani da kuma aiwatar da wadannan abubuwa ne za mu samu Sallah mai kyau.
Mu kwana nan.