✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Tsohuwar Kwamishinan Lafiyar Bauchi ta rasu

Dakta Zuwaira wadda ta taba rike mukamin kwamishinan lafiya na jihar Bauchi ta rasu ranar Litinin da safe a hadarin mota.

Tsohuwar Kwamishinar Lafiya ta Jihar Bauchi, Dakta Zuwaira Hassan Ibrahim, ta rasu a wani hatsarin mota da ya ritsa da ita a kan titin Jos zuwa Bauchi.

Marigayiyar ita ce Shugabar Sashen Magunguna na Asibitin Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi.

‘Yan uwanta sun tabbatar wa da Aminiya cewa hadarin ya faru ne yankin Zaranda Gari a ranar Litinin da safe.

Ta fara aiki a asibitin a ranar 1 ga watan Nuwambar 2020.

Dakta Zuwaira ta yi Kwamishinar Lafiya ne karkashin mulkin tsohon gwamnan jihar, Barista Mohammed Abdullahi Abubakar.

Za a kuma jana’izarta a masallacin juma’a na asibitin koyarwa na Abubakar Tafawa Balewa, da ke Bauchi.

Dakta Zuwaira ta rasu ta bar mijinta da ‘ya’ya uku.

Wakilinmu bai samu tattaunawa da babban Daraktan asibitin na ATBU-TH, saboda rashin daga wayarsa da ya yi.