Kotu ta yanke wa mata tsohuwa da ta kashe mijinta saboda abincin bikin murnar ranar haihuwarta hukuncin daurin shekara 18.
Penelope Jackson mai shekara 66 ta daba wa mijin nata wuka a kirji har sau uku, wanda hakan ya yi sanadin shekawarsa lahira, a gidansu da ke titin Parsonage Berrow, a yankin Somerset da ke kasar Birtaniya.
- Rahoton Daily Trust ya sauya rayuwar makaho a Kano
- ’Yan kwallon Najeriya 3 da ke daukar sama da miliyan 30 a sati
Ta amsa a gaban kotu cewa ita ce ta daba masa wuka a ranar 13 ga watan Fabrairun 2021, kan sabanin da suka samu kan abincin bikin zagayowar ranar haihuwarta, amma ba ta kashe shi ba.
Bayan da alkalin kotun, Mai Shari’a Judge Martin Picton, ya tambaye ta sau nawa ta daba wa mijin nata wuka wuka ta amsa cewa sau daya ne.
An jiyo muryar Mista Jackson, wanda tsohon hafsan soja ne mai mukamin Laftanar-Kanar, a lokacin da ya kira lambar neman agaji ta 999.
Tsohon mai shekara 78 a duniya, an kashe shi ne da wukar yanke-yanke da ake amfani da ita a dakin girki.