✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsohuwa da saurayin jikarta

Wani saurayi ne ya ga wata budurwa ya ji yana sonta da aure, sai ya tambaya aka shaida masa cewa tana hannun kakarta ce. Sai…

Wani saurayi ne ya ga wata budurwa ya ji yana sonta da aure, sai ya tambaya aka shaida masa cewa tana hannun kakarta ce. Sai ya je gidan don su gaisa, ya shaida mata cewa: “Inna, Maryam ce na gani nake so da aure.” Sai tsohuwa ta ce: “A’a yaro an ba da ta.” Da zai tafi sai ya ciro damen kudi sababbi ya mika mata ya ce ta sayi goro. Da ta ga kudi cus, sai ta ce: “tsaya yaro, ka dan gidan wane ne?” Ya ce shi dan gidan Malam Haruna ne. Ta ce na wajen Malam Saleh, ya ce, eh. Ta ce: “Allah Sarki! Malam Saleh mutumin kirki ne, lokacin da muke yara idan muka ja fada shi ke tare mana!”
Daga Anisa Adamu Abdullahi Daura, 07067716102