Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi a Najeriya (NDLEA), ta cafke wata tsohuwa mai shekaru 80 tare da jikarta ’yar shekara 19 dauke da hodar ibilis mai nauyin giram dubu 192 a Akure, babban birnin Jihar Ondo.
Daraktan yada labarai da wayar da kan al’umma na hukumar, Mista Femi Babafemi ne ya bayyana hakan ga manema labarai ranar Laraba a Abuja.
Babafemi ya ce, hukumar ta kuma samu nasarar cafke wasu ’yan mata biyu masu sayar da haramtattun kwayoyi masu gusar da tunani da suka hada da hodar ibilis da hodar heroin da methamphetamine da tramadol da swinol da kuma skuchies.
Daraktan ya ce, hukumar ta yi nasarar kama ababen zargin ne yayin gudanar da wani rangadi a ranar 2 ga watan Mayun 2021.
Kazalika, ya ce bayan nasarar kwace hodar ibilis me nauyin giram dubu 192, sun kuma yi nasarar kwato miyagun kwayoyi da dama a hannun mutanen da ake zargi da aikata laifin.
An dai kama tsohuwar da jikarta ce da misalin karfe 6:30 na safiyar ranar Lahadi a layin Ayeyemi da ke Karamar Hukumar Akure ta Kudu.