Tsohon gwarzon tsere na duniya, Abdalelah Haroun, dan Kasar Sudan da ya wakilci kasarsa a Qatar, ya mutu a hatsarin mota.
Hukumar kula da wasannin guje-guje da tsalle-tsalle ta duniya ce ta sanar da rasuwar tsohon zakaran mai shekara 24 a ranar Asabar.
Haroun wanda ya kasance tsohon zakara a duniya a kan gudun mita 400, ya lashe kyautar zinare a gasar wasannin Asiya ta 2018 da kuma gasar wasannin motsa jiki ta Asiya ta 2015.
Baya ga azurfar da ya lashe a wasannin motsa jiki ta cikin gida a cikin 2016, mamacin ya samu kyautar tagulla a Gasar Zakarun Duniya ta 2017 da aka gudanar Landan.
Haroun ya samu cancantar zuwa kasar Qatar ne a shekarar 2015 kuma yana daya daga cikin ’yan wasan da suka wakilci nahiyar Afirka.