✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsohon wakilin BBC Mato Adamu ya riga mu gidan gaskiya

Za a gabatar da sallar jana’izarsa a gobe Asabar da misalin karfe 11 na safe.

A Yammacin wannan Juma’ar ce Allah Ya yi wa gogaggen dan jaridar nan da ya yi aiki da sashin Hausa na gidan Rediyon BBC, Alhaji Mato Adamu rasuwa a Gombe.

Mato Adamu mai shekaru 60 a doron kasa ya rasu ne bayan ya yi fama da ’yar gajeruwar jinya kamar yadda wakilinmu ya ruwaito.

Kafin rasuwarsa, ya taba zama mai bai wa Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya na Jihar Gombe shawara na musamman kan harkokin yada labarai.

Za a gabatar da sallar jana’izarsa a gobe Asabar da misalin karfe 11 na safe a Asibitin kwararrun na Jihar Gombe.