Tsohon Babban Hafson Sojin Kasa na Najeriya, Laftanar-Janar Azubike Ihejirika ya shiga jam’iyyar APC mai mulki.
- Shugaban Kwamitin Rikon APC na kasa, Mai Mala Buni ne ya karbi Ihejirika a cikin jam’iyyar.
- ‘Babu mahalukin da ya isa ya karya Gwamnatin Buhari’
- Saniya ta kai wa marasa lafiya farmaki a asibiti
- Shin malaman Kano za su iya ja da Abduljabbar?
Mai magana yawun Buni, Mamman Mohammed ya ce Shugaban Kwamitin tsare-tsaren Jam’iyyar kuma Gwamnan Jigawa, Abubakar Badaru da Shugaban Kwamitin Tuntuna na Jam’iyyar Hon. Farouk Adamu Aliyu ne suka gabatar da Ihejirika ga Buni ranar Juma’a.
“Shigowar Janar Ihejirika zai kara wa jam’iyyarmu karsashi a Jihar Abiya da ma daukacin yankin Kudu maso Gabas.
“Babban abin murna ne ganin Janar Ihejirika da wasu fitattun ’ya’yan yankin Kudu maso Gabas suna shigowa jam’iyyar domin kawo yankin kusa da Gwamnatin Tarayya.
“Muna sa ran ganin kara kafuwar APC a yankin,” inji Buni.