✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Tsohon shugaban Nijar Tandja Mamadou ya rasu

Tandja Mamadou ya rasu a birnin Yamai yana da shekaru 82.

Tsohon shugaban kasar Nijar, Tandja Mamadou ya rasu a birnin Yamai yana da shekaru 82.

Gidan talabijin na Gwamnatin kasar Nijar ne ya sanar da rasuwar a ranar Talata da misalin karfe 8 na dare.

Sanarwa ta kara da ce wa, gwamnatin kasar ta bayar da hutun kwanaki uku na makokin rasuwar tsohon shugaban.

Shugaban kasar mai ci Mahamadou Issoufou, ya mika sakon ta’aziyarsa ga daukacin al’ummar kasar da ’yan uwa da iyalan marigayin tsohon shugaban a madadin gwamnati kasar.

Al’ummar kasar da dama na nuna alhininsu dangane da rasuwar tsohon shugaban kasar wanda suka fi kira da ‘Baba Tandja’.

Tsohon soja ne wanda ya mulki Nijar daga Disamban 1999 zuwa Fabarairun 2010 kuma yana daga cikin rukunin sojojin da suka yi juyin mulki a shekarar 1974.

Tarihi ya nuna an haifi marigayi Tandja Mamadou a shekarar 1938 a garin Mainé-Soroa da ke jihar Diffa, kuma ya zama shugaban kasar Nijar a 1999.

Kazalika, an kuma sake zabensa a 2004, daga bisani sojoji karkashin jagorancin Janar Salou Djibo suka yi masa juyin mulki a ranar 18 ga watan Fabrairu 2010 yayin da takaddama ta kaure kan batun Tazarcensa.