Tsohon Darakta Janar na Hukumar NCAA mai Kula da Zirga-Zirga Jiragen Saman Kasar, Kyaftin Mukhtar Usman ya riga mu gidan gaskiya.
Marigayin ya rasu ne ranar Talata bayan ya shafe shekaru 63 a a duniya.
Shugaban Kungiyar Manyan Ma’aikatan Jigilar Jiragen Sama, Illitrus Ahmadu ne ya tabbatar wa da ‘yan jarida rasuwar marigayin da safiyar Laraba a wata tattauna wa da ya yi da manema labarai ta wayar tarho.
- Kisan Zabarmari: Majalisa ta shawarci Buhari a kan Hafsoshin Tsaro
- Coronavirus ta sake kashe mutum 3 a Najeriya
Rahotonni sun ce marigayi Muhtar ya rasu ne a daren ranar Talata a wani asibiti a garin Zariya na jihar Kaduna bayan ya yi fama da gajeriyar jinya.
A watan Oktoban 2014 ne aka nada shi a matsayin Darakta Janar na Hukumar NCAA inda ya jagorance ta na tsawon shekaru biyar.
Ya kuma mika wa Kyaftin Musa Nuhu ragamar jagorancin Hukumar a watan Oktoban 2019.
Kazalika, ya taba rike mukamin Kwamishina a Hukumar Binciken Hatsarin Jiragen Sama ta Kasa.