Tsohon Shugaban Asibitin Koyarwa na Mallam Aminu da ke Kano, Farfesa Abdulhamid Isa Dutse, ya riga mu gidan gaskiya a Yammacin jiya na Litinin bayan ya yi fama da ‘yar gajeriyar rashin lafiya.
Wani makusanci ga iyalan Marigayin ya sanar da cewa za a yi jana’izar sa da misalin karfe 10 na safiyar Talata a masallacin Alfurqan da ke Nasarawa GRA.
Tun bayan kwantar da shi a sashen ba da kula wa ta musamman na babban asibiti, an rika barar addu’o’in al’umma da su nema masa samun waraka a wurin Mai Duka inda bayan ‘yan sa’o’i kadan ya ce ga garinku nan.
An haifi marigayi Farfesa Dutse a watan Dasumban 1960 a Unguwar Gini da ke tantagwaryar birnin Kano, inda ya yi karatunsa a Firamaren Kwalli a shekarar 1966 gabanin ya koma Makarantar Firamare ta Magwan.
A shekarar 1972 ne ya samu gurbin karatu a Makarantar Government College Kano wadda a yanzu ake kiranta da Kwalejin Rumfa (Rumfa College).
Daga nan Farfesa Dutse ya samu gurbin karatun Likitanci a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar, inda ya samu nasarar kammala karantun kwarewa a aikin Likitan Yara a shekarar 1982 a matsayin dalibin da ya fi kowanne hazaka da samun sakamako mafi kyawu cikin sa’o’insa a lokacin.
Gabanin ajali ya katse masa hanzari, ya rike mukamai daban-daban a Hukumar Kula da Asibitoci ta Jihar Kano da wasu wuraren na daban.