✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsohon Sakataren Gwamnati ya sauya sheka zuwa PDP a Katsina

Na lura ni da magoya bayana ba mu da bakin fada a ji a Jihar Katsina.

Wani babban jigo a jam’iyyar APC a Jihar Katsina, Dakta Mustapha Inuwa ya sauya sheka zuwa jam’iyyar PDP.

Daktan ya sanar da hakan ne a ofishin yakin neman zabensa a garin Katsina bayan wata ganawa da ya yi da dubban magoya bayansa a ranar Lahadi.

Dakta Inuwa wanda shi ne tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar a wa’adin farko na Gwamna Aminu Masari, ya nemi takarar Gwamnan Jihar a karkashin jam’iyyar APC amma ya sha kaye a hannun Dakta Dikko Radda a zaben fidda gwani.

Ana gama zaben da ya sha kaye, sai ya sanar da mika wuya, tare da ayyana tafiya tare da Radda a wani taron ‘yan jarida da ya kira.

Daga baya kuma dangartaka ta yi tsami tsakanin bangarorin ‘yan siyasar biyu, inda suka rika jefa wa juna maganganu wanda ta sa manya-manyan jam’iyyun NNPP da PDP da kuma na LP suka shiga zawarcinsa.

Kwatsam sai a ka ji shi a PDP, jam’iyyar da ya bari tare da sauya sheka zuwa a APC gabannin Zaben 2015.

Cikin dalilan da ya bayar na barin APC shi ne cewa, ya lura shi da magoya bayansa ba su da bakin fada a ji a jihar.