Tsohon Ministan Yada Labarai a zamamin tsohon Shugaban Kasa, Olusegun Obasanjo, Ikira Aliyu Bilbis, ya lashe kujerar Sanatan Zamfara ta Tsakiya.
Bilbis ya sami nasarar ce a zaben da aka karasa na ranar Asabar, inda ya doke tsohon Sanatan da ya taba hawa kujerar, Kabiru Marafa.
Ikira dai ya sami kuri’a 102,866 ne, inda ya doke Sanata Marafa mai kuri’a 91,216 .
A wani labarin kuma, dan takarar PDP, Ahmad Kabiru, ya lashe kujerar Majalisar Wakilai daga mazabar Gusau?Tsafe.
Bugu da kari, shi ma Sulaiman Gummi, wanda ya yi wa PDP takarar kujerar Majalisar Wakilai a mazabar Gummi/Bukkuyum, ya lashe zaben, kamar yadda Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta bayyana.