✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsohon mai laifi ya fasa gidan Fasto ya sace kudin sadaka

Ana tuhumar wani tsohon dan fursuna, mai suna Kenneth Ejiofor, wanda bai dade da fitowa daga kurkuku ba da fasa gidan wani fasto, inda ya…

Ana tuhumar wani tsohon dan fursuna, mai suna Kenneth Ejiofor, wanda bai dade da fitowa daga kurkuku ba da fasa gidan wani fasto, inda ya yi awon gaba da dukiyar sadaka mallakar cocin.

Aminiya ta samu labarin cewa, tun  farko Kenneth yana zaune ne tare da Fasto Samuel Orji. Kuma a ranar 30 ga Satumban da ya gabata, sai ya fasa gidan nasa, lokacin da faston ke wajen bauta a coci, ya sace dukiyar sadaka da katin ATM biyu, mallakar cocin.

Wata majiya ta ce, Kenneth ya samu sabani ne a tsakaninsa da Fasto Orji, wanda ya kore shi daga gidansa. Dalili ke nan ya sanya tsohon fursunar ya fusata, ya bari sai da faston ya tafi coci, sai ya fasa gidan ya aikata barnar.

Aminiya ta samu bayanin cewa lokacin da ya shiga gidan, ya tattara wasu kudaden cocin da suka kai Naira 11,000, sannan ya sake tafiya da wasu kudin da ba a gama tantance kimarsu ba.

Da yake yi wa ’yan sanda bayani, Fasto Orji ya ce tun farko yayan Kenneth ne ya roke shi ya yi masa addu’ar shiriya, wanda dalili ke nan ya amince ya ajiye shi a gidansa, amma sannu a hankali sai aka rika lura da cewa wasu kayayyaki suna salwanta a gidan. “Daga kauye yayan nasa ya taho da shi Legas amma saboda munin halayensa, shi ya sanya ya kasa zama tare da shi. Don haka sai ya roke ni da in bar shi ya zauna a tare da ni domin in rika yi masa addu’ar shiriya,” inji faston.

Ya ci gaba da cewa, “Bayan mun amince da shi, matata kan dafa abinci ta ba shi, amma bayan ya cinye sai ya saci nama daga tukunya. Da matata ta ga haka sai ta sayo makulli ta rika kulle kicin amma duk da haka sai ta lura cewa ba a daina sata ba kuma wasu lokutan har da kudi ake sacewa, ashe ba mu sani ba, Kenneth yana da wani mabudi da yake amfani da shi.

“Aikinsa shi ne kawai ya rika debo mana ruwa sau daya a cikin kwana biyu. Ranar wata Asabar ba mu da ruwa a gidan, sai  dan kadan da ya rage a kicin. Shi ne sai ya yi amfani da wannan ruwa da ya rage mana ya yi wanka. Lokacin da na kalubalance shi kan haka, sai ya ce yana fa ganin girmana don haka in girmama kaina ni ma. Ganin haka sai na fusata, na ce masa ya tashi ya bar mini gidana,” inji faston.

Ya ce “A ranar Lahadi, bayan mun tafi coci sai ya dawo ya balle kofar gidan ya bude falo da wani mabudinsa ya kwashe Naira dubu 11, ya kwashe wasu kudin sadaka na cocin, wadanda ba mu kai ga kidaya su ba, ya hada da katin ATM guda biyu.”

A nasa bangaren Kenneth ya ce shi tsohon fursuna ne amma ya musanta cewa ya yi sata gidan faston. An gurfanar da shi a gaban Kotun Majistare da ke Ogba, inda aka tuhume shi da aikata sata da ta da zaune -tsaye amma ya musanta tuhumar.

Mai gabatar da kara ya fadi a takardar tuhumar cewa: “Kai Kenneth Ejiofor, a ranar 30 ga Satumba, daidai misalin karfe 10:30 na dare, a kan Titin Awoni Murphy, daura da Titin Haruna College, Ogba-Legas, ka fasa kyauren gida, ka shiga cikin falo kuma ka yi sata, ka yi barazana ga masu gidan, wanda hakan ka aikata da nufin cutar da masu gidan. Wannan laifi da ka aikata, zai sa a hukunta ka a karkashin sashi na 307 na Kundin Shari’ar Laifuffuka na Jihar Legas.

“Haka kuma kai Kenneth Ejiofor, a wannan rana kuma a daidai wannan lokaci, a wannan adireshi da aka ambata, ka saci  Naira 11,500 da katin ATM na Bankin Zenith, kayan duka na Fasto Samuel Orji, wanda haka babban laifi ne da ya saba wa sashi na 280 na Kundin Shari’ar Laifuffuka  na Jihar Legas.”

Majistare W. A. Salami ya ba da wanda ake tuhuma a hannun beli a kan Naira dubu 100 tare da kawo mutum  biyu da za su tsaya masa. Daga bisani kuma ya dage shari’ar zuwa ranar 21 ga Nuwamba mai zuwa.