✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Tsohon mai kamfanin Twitter ya kaddamar da sabon shafin sada zumunta

A yanzu haka na da masu amfani da shi fiye da 30,000.

Mutumin da ya kirkiri manhajar sada zumunta ta  Twitter, ya kuma shugabanci kamfanin Jack Dorsey, ya kaddamar da sabon shafin sada zumunta mai suna Bluesky.

Wannan dai na zuwa ne kasa da mako guda bayan Mai Kudin Duniya, Elon Musk ya saye kamfanin.

Sabon dandalin da ke kan matakin gwaji yanzu haka na da masu amfani da shi fiye da 30,000, kwana biyu kacal bayan sanar da bullarsa.

Rahotanni na nuna cewa shafin Bluesky ya zo da sabon tsarin da ya sha bamba da sauran shafukan sada zumunta, inda yake bai wa masu amfani da shi damar tsara shafukansu yadda suke so.

Baya ga haka kuma, yana neman ma’aikata a bangaren tsara manhajar waya, da masu kirkirar zane, da sauran manajoji daban-daban.

Dorsey dai guda ne daga shugabannin da suka samar da shafin Twitter shekaru 17 da suka gabata, inda ya jagorance shi na takaitaccen lokaci, kafin dawowarsa a shekarar 2015 zuwa 2021, lokacin da ya ajiye aikin baki daya.