Tsohon Sakataren Yada Labarai na jam’iyyar PDP ta kasa, Cif Olisa Metuh, yanzu haka yana ganawa da Shugaban Kasa, Bola Tinubu a fadar Aso Rock.
Metuh, wanda ya taba rike mukamin a PDP lokacin da APC ta kawo karshen mulkin jam’iyyarsa na shekara 16 a 2015, ya isa fadar ne tare da tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Anyim Pius Anyim.
- NEMA ta bayyana jihohi 14 da za su iya fuskantar mummunar ambaliya a makon nan
- Alhazan Najeriya na fargabar komawa Madina
A baya dai, duka su biyun sun shahara wajen yin adawa ga APC gabanin zaben 2015. An fara tattaunawar ce da misalin karfe 2:00 na ranar Laraba.
Shi kuwa Anyim, wanda kuma tsohon Shugaban Majalisar Dattijai ne ana ganin ya yi wa APC aiki a Jihar Ebonyi a zaben da ya gabata.
A watana Oktoban 2022 ne kuma Metuh ya bayyana ficewarsa daga PDP da kuma duk wata siyasar jam’iyya.
Wannan ne dai karo na farko da aka ga Metuh a fadar tun lokacin da tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan ya bar mulki.
A baya dai tsohon Kakakin ya fuskanci tuhuma kan zargin almundahanar wasu kudade, zamanin tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.