Tsohon hadimin gwamnan Jihar Kano na musamman kan yada labarai a kafofin sadarwar zamani, Salihu Tanko Yakasai, ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar gwamnan Jihar Kano a zaben 2023 da ke tafe.
Yakasai ya bayyana hakan ne cikin wani sako da ya wallafa ranar Talata a shafinsa na Twitter.
- Mutum 8 sun mutu bayan kwankwadar barasa a Iran
- Ba za mu taba bari ’yan bindiga su samu sukuni ba—Sarkin Musulmi
Tsohon hadimin gwamnan wanda aka fi sani da Dawisu ya ce zai ayyana takararsa a hukumance ranar Juma’a mai zuwa.
Wannan na zuwa ne makonni bayan ficewarsa daga jam’iyyar APC, inda ya sauya sheka zuwa jam’iyyar PRP.
Idan ba a manta ba dai a watan Fabrairun 2021 ne gwamna Ganduje ya sauke shi daga mukaminsa bisa dalilinta na cewa Yakasan na maganganun da ba su kamata ba da kuma sukar shugaban kasa Muhammadu Buhari.