✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsohon gwamnan Jihar Kaduna ya rasu

Allah ya yi wa tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Iya bayis Mashal Mukhtar Muhammed mai ritaya rasuwa. Marigayin wanda ya mulki tsohuwar jihar Kaduna daga shekarar…

Allah ya yi wa tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Iya bayis Mashal Mukhtar Muhammed mai ritaya rasuwa.
Marigayin wanda ya mulki tsohuwar jihar Kaduna daga shekarar 1977 zuwa 1978 ya rasu ranar daren Lahadin da ta gabata yana dan shekara  73 a duniya.
Kaninsa, Aminu Dalhatu ya shaida wa Aminiya cewa marigayin ya rasu a asibitin birnin Landan bayan gajeruwar rashin lafiya.
Dalhatu ya bayyana cewa za a dawo da gawar marigayin gida Najeriya inda za a yi masa jana’iza.