✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsohon Golan Najeriya ya rasu

Tsohon golan Najeriya Raymond King ya rasu a ranar Litinin da ta gabata.  Ya rasu ne yana da shekara 52. Kamar yadda abokinsa Taju Disu…

Tsohon golan Najeriya Raymond King ya rasu a ranar Litinin da ta gabata.  Ya rasu ne yana da shekara 52.

Kamar yadda abokinsa Taju Disu da suka yi kwallo tare a kungiyar Flying Eagles ya sanar, ya ce King ya rasu ne a Asibitin Kwarru na Jami’ar Jihar Legas (Lagos State University Teaching Hospital) bayan an yi masa canjin asibitin da aka kwantar da shi na Ikorodu General Hospital tun da farko.  Ya kama wa Flying Eagles gola ne a tsakanin shekarar 1979 zuwa 1980. Ya rasu ne bayan ya kamu da cutar shanyewar varin jiki (stroke).  Raymond King dai ya fito ne daga Jihar Ogun.