✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsohon Golan ‘Flying Eagles’ John Felagha ya rasu

Tsohon mai tsaron ragar kungiyar kwallon kafa ta Flying Eagles John Falegha ya rasu. Hukumar Kwallon Kafa ta Najeriya (NFF) ta ce John Falegha ya…

Tsohon mai tsaron ragar kungiyar kwallon kafa ta Flying Eagles John Falegha ya rasu.

Hukumar Kwallon Kafa ta Najeriya (NFF) ta ce John Falegha ya rasu ne a ranar Lahadi 30 ga watan Agustan 2020 a kasar Senegal.

Falengha golan ‘yan kungiyar kwallon kafa ta Najeriya ‘yan kasa da shekaru 17 da ‘yan kasa da shekaru 20 ya rasu yana mai shekaru 26.

Hukumar ta NFF ta aike da sakon ta’aziyar rasuwarsa ga iyalansa ta kafar sadarwa ta Twitter a ranar Litinin.