Fadar Vatica ta tabbatar da cewa tsohon Fafaroma, Benedict XVI ya mutu yana da shekara 95 a duniya.
Rasuwar tasa ta ranar Asabar na zuwa ne ’yan kwanaki bayan Fafaroma Francis ya yi kira ga Kiristoci da su yi masa addu’a saboda jikinsa ya yi zafi.
A cewar fadar ta Vatica, Benedict, wanda shi ne Fafaroma na farko dan asalin kasar Jamus cikin sama da shekara 1,000, ya rasu ne a gidansa da ke Mater Ecclesiae.
Ya kasance a cikin gidan dai tun lokacin da ya sauka daga mukamin nasa a shekarar 2013.
Sai dai fadar ba ta bayyana ainihin abin da ya yi sanadin mutuwar tasa ba, inda ta ce lafiyarsa ta tabarbare ne saboda tsufa da shekaru.
Masu ra’ayin rikau a cocin ma kallon tsohon Fafaroman a matsayin jagoransu, inda har wasu daga cikinsu suka ki yarda su amince da Francis a matsayin sabon Fafaroman.
Sun dai soki lamirin Fafaroma Francis kan yadda ya rungumi masu rajin auren jinsi daya a cocin, da kuma ’yan darikar Katolikan da suka yi saki sannan suka sake yin aure daga wajen cocin. Sun ce duka wadannan sun saba wa ginshikan da aka san cocin da su.