✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsohon dan kwallon Najeriya ya rasu

Allah Ya yi wa tsohon dan kwallon Red Debils da yanzu ake kira Super Eagles Dejo Fayemi rasuwa. Ya rasu ne a gidansa da ke…

Allah Ya yi wa tsohon dan kwallon Red Debils da yanzu ake kira Super Eagles Dejo Fayemi rasuwa. Ya rasu ne a gidansa da ke Ibadan yana da shekara 83 a ranar Talatar da ta gabata bayan ya yi fama da rashin lafiya.

Kamar yadda rahotanni suka nuna Fayemi yana daga cikin ’yan kwallon farko da suka taba ziyartar Ingila kuma suka buga wasa a filin kwallon Arsenal da aka fi sani da Highbury a wani wasan sada zumunta jim kadan bayan Najeriya ta samu ’yancin kai.
Tsohon dan kwallon ya yi wa Eagles kwallo ne a tsakanin shekarar 1959 zuwa 1965.
Ya samu nasarar zura wa Eagles kwallaye bakwai kuma kwallonsa ta karshe ita ce wacce ya zura a ragar Moroko a shekarar 1964 a wani wasan sada zumunta inda Maroko ta lallasa Najeriya da ci 2-1.
Marigayin ya taimaka wa kulob din Ibadan Lions wajen lashe kofunan kalubale a shekarar 1959 da 1961 bayan an doke kulob din a wasan karshe na cin kofin kalubalen a shekarar 1960.
Tuni masana harkar kwallo a ciki da wajen Najeriya suka aika sakonnin ta’aziyyarsu ga iyalan mamacin a kan rashin da aka yi.