✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Tsohon dan kwallon Najeriya Justice Christopher ya rasu

Justice Christopher ya yanke jiki ya fadi a safiyar Laraba a garin Jos, Jihar Filato

Tsohon dan wasan tsakiya a tawagar kwallon kafa ta Super Eagles ta Najeriya, Justice Christoper, ya riga mu gidan gaskiya.

A safiyar Laraba Justice Christopher wanda ke zaune a garin Jos na Jihar Filato, ya rasu yana da shekara 40, bayan ya yanke jiki ya fadi.

Christopher ya fara buga wa tawagar Super Eagles wasa ne a 2001; sau 11 yana buga mata wasanni kuma yana cikin tawar ’yan wasan da suka wakilci Najeriyar a gasar Kofin Duniya na Korea/Japan 2002.

Makusantan tsohon dan wasan tsakiyar sun shaida wa Aminiya cewa ya jima yana fama da cutar hawan jini, amma mara tsanani.

A ranar Talata an gan shi tare da wasu abokansa cikin nishadi, babu wata alamar damuwa ko lalura a tare da shi.

Wakilinmu ya ce abokan nasa sun kadu matuka da samun labarin rasuwar tasa a safiyar Larabar da abin ya faru.

Tsohon dan wasan tsakiyar ya fadi ne a otal din Gwolshe, da ke daura da titin Tudun Wada Ring a garin na Jos.

Kawo yanzu dai Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Filato ba ta fitar da sanarwar rasuwar tsohon dan kwallon ba a hukumance.

Amma tuni aka kai gawarsa zuwa Asibitin Kwararru na Filato domin gudanar da bincike.