✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsohon dan kwallon AC Milan ya zama Magajin Gari

A ranar Asabar da ta wuce ne aka zabi tsohon dan kwallon kulob din AC Milan na Italiya Kakha Kaladze a matsayin Magajin Garin Tbilisi…

A ranar Asabar da ta wuce ne aka zabi tsohon dan kwallon kulob din AC Milan na Italiya Kakha Kaladze a matsayin Magajin Garin Tbilisi da ke kasar Georgia.

dan kwallon wanda ya taba buga wa kulob din AC Milan kwallo ya samu nasarar lashe zaben ne da kashi 51 daga cikin 100 na yawan kuri’un da aka kada.

dan shekara 39 ya buga wa Milan kwallon ne a tsakanin shekarun 2001 zuwa 2010 kuma ya samu nasarar lashe kofuna biyu na Gasar Zakarun Kulob na Turai (Champions League) a yayin da yake wa kulob din kwallo.  Sannan ya buga kwallo ne a matsayin mai tsaron baya (Defender).

Sannan dan kwallon ya taba buga wa kulob din Dynamo Kieb da na Dinamo Tbilisi kwallo sannan ya taba rike matsayin kyaftin a kungiyar kwallon kafa ta Georgia kafin ya yi ritaya a shekarar 2012.

 Bayan ya yi ritaya ne sai ya shiga harkar siyasa inda ya rike mukamin Minista.

A wannan karo ne ya shiga takarar zama Magajin Garin Tbilisi shi da wani shararren mai kudi kuma dan kasuwa, inda ya samu nasara a zaben da kashi 51 cikin 100.

Kakha dai yana daga cikin tsofaffin ’yan kwallon Milan biyu da suka shiga harkar siyasa bayan sun yi ritaya a kwallo. Na biyun shi ne George Weah,. dan asalin Laberiya da yanzu haka ake fafatawa da shi a zaben zama shugaban kasar Laberiya.