Wani tsoho mai kimanin shekara 65 ya shiga komar ’yan sandan a Jihar Ogun bayan da aka zarge shi da yi wa yarinya ’yar shekara 10 fyade.
A cewar mai magana da yawun Rundunar ’Yan sandan Jihar Ogun DSP Abimbola Oyeyemi rundunar ta kame tsohon mai suna Sulaiman Rauf ne, bayan da mahaifin yarinyar Fahinhun Mathew ya shigar da kara a ofishin rundunar da ke garin Idiroko a jihar, inda ya ce tsohon ya aiki yarinyar ce bayan da ta kai masa sakon sai ya yaudare ta ya shigar da ita dakinsa inda ya yi lalata da ita. “Nan take ta sanar wa iyayenta abin da tsohon ya yi mata bayan da ta fito, kana a binciken da muka yi masa ya amsa laifinsa, inda ya ce bai san abin da ya sanya shi ya aikiata hakan ba,” inji Kakakin ’Yan sandan Jihar Abimbola Oyeyemi.
Ya ce, tuni aka garzaya da yarinyar asibiti domin bincikar lafiyarta a daidai lokacin da Kwamishinan ’Yan sandan jihar Alhaji Bashir Makama ya ba da umarnin a tasa keyar wanda ake zargin zuwa sashen yaki da cin zarafin yara na rundunar.