Kayan hadi:
. Dankalin Turawa
. Nikakken nama
. Man gyada
. Sinadarin dandano
. Kayan kanshi
Yadda ake yi:
Uwargida za ki samu nikakken nama sai ki hada shi da kayan kanshi da sinadarin dandano. Idan ya hadu sai ki gutsira ki fadada shi yadda zai yi falan-falan sai ki ajiye shi a gefe.
Sannan ki dauko dankalinki irin manyan nan sai ki fere shi sannan ki yanka shi a kwance ma’ana kamar kwabo.
Sai ki dauko tsinken tsire ki jera dankalin nan naki a jiki, tare da hadadden nikakken naman.
Idan kika sa dankali a jikin tsinken sai ki dauko wannan nikakken naman ki sa shi a jiki daidai fadin dankalin sannan sai ki sake sa dankalin sai kuma ki sa naman.
Haka za ki yi ta yi har sai tsinken ya cika.
Amma ki tabbatar dankalin da kika yanka ya kasance guda daya ma’ana sai kin gama da guda daya sanann za ki sake yanka wani don kada ya hargitse wajen jera dankalin a jikin tsinken.