Dangane da haka ni a tawa tsinkayar akwai abubuwa kamar guda hudu da za mu iya yi ko matakan da za mu iya bi domin kai wa ga tudun mun tsira.
Abu na farko shi ne mu tabbata in lokacin zabe ya yi mun zabi wadanda suka dace da zamanin da muke ciki, ma’ana, wadanda mun tabbatar za su agaza wajen raya al’umma ba wadanda za su kashe ta ba. Su wane ne wadannan mutane? Ba zan so na ji wani na cewa ai Shugaba Buhari ya ishe mu ba, Shugaba Buhari itace ne daya, kuma ba yadda za a yi itace daya ya kasance gwanja ko kasurgumin daji. Dole a samu wasu irinsa su kama, su agaza, su kuma tabbatar ba a samu lauje cikin nadi ba. Ba zai taba yiwuwa ba a ce ba a da mutanen da za su iya fitar da kasar nan daga cikin halayen da take ciki. Har yanzu akwai na kwarai a cikin al’ummarmu. Har yanzu akwai masu kishin ci gaban al’umma ta kowace irin fuska. Suna nan jingim! Su ya dace mu fita nema ko da ba sa siyasar da ake yi yanzu, domin jawo su, su maye gurbin wadanda muke ta faman shan wahalarsu a halin yanzu.
Ke nan ba jam’iyyar siyasa ya kamata mu damu da ita ba a hairin wannan hali da muke ciki, a’a, zabo yardaddun mutane da za su fitar da A’i daga sana’ar rogon da take ta fama ita, kuma na tabbata akwai su, ba a dai fita nema ba ne!
Sai dai a tuna idan har mun samo irin wadannan mutane, idan mun nemo su daga cikin tarin al’ummar da muke da su, muka kuma amince musu, to sai mu mayar da hankali wajen tallata su domin a zabe su, mu kuma tabbata ba a yi mana sakiyar da ba ruwa ba, a lokacin zaben nasu. Sai dai ba nan za mu tsaya ba. Idan har kuma mun zabe su, mu tabbata mun bar su domin su yi mana aikin raya kasa ba aikin raya mana tukwananmu ba. Ma’ana, yadda muke biye wa son rai in mun yi zabe ta hana zababbun wakilai ko jami’ai su tsaya su yi aiki yadda ya kamata, muna biye da wadanda muka zaba domin su ba mu taro ko sisi ko kuma su biya mana bukatanmu, in ya so aikin raya kasa ko oho, yana da cikin matsalolin da ke sa ’yan siyasa ke yi mana wa-ka-ci-ka-tashi. Mu bar su da dukiyar kasa da dukiyarmu, su yi aikin da aka tanada, wanan shi ne zai taimaka wajen kawo abincin karin kumallo ga wanda ke bukata da aikin yi ga wadanda suke bukata ko kuma zaman lafiya a cikin kasa. Idan mun daure muka hadiye kwadayi, to za mu iya matsa wa wadanda muka zaba su yi wa al’umma aiki ba wandaka ba!
Haka kuma ya dace mu kasance masu sa ido ba wai sa’idawa ba game da yadda ake mulkarmu ko ake gudanar da lamuran dukiyarmu a kowane mataki na rayuwa. Wannan aikinmu ne domin mu ne masu zabe da kuma kulawa. A tuna wanda aka zaba ba gunki ba ne ko wani dodo, idan mun dage wajen ganin an yi yadda ya dace, to dole za a yi, idan kuma mun mika ragamar mulkin ga wadansu, muka sa kwadayi da rashin kishin kasa a rayuwarmu, to duk bala’in da ya auka mana, mu muka ja wa kanmu. Hausawa na cewa sai bango ya tsage kadangare ke samun wurin shiga, Daga karshe kuma, Hausawa na cewa ba a fafe gora ranar tafiya. Shekarar zabe ta riga ta karato ba, nan da badi lokacin da za a yi zabe, ba wani lokaci mai tsawo ba ne, mu fara shiri tun yanzu, ba sai lokacin zabe ba! Me nake nufi? Shin ina wadanda muka zaba a halin yanzu, ai suna nan ba su sauka ba, me zai hana mu fara sa ido kan su tun yanzu. Mu bi duk wani kansila ko ciyaman ko kantoma ko dan Majalisar Jiha ko Gwamna ko dan Majalisar Tarayya ko Sanata ko Shugaban kasa mu ce ina awalajar dimokuradiyyar da aka yi mana alkawari daga shekarar 2015? Wane aiki kuka yi da za mu sake dora ku bisa wannan mukami ko mu sake ba ku wani sabo don ku ci gaba da mulki? Mu tambaye su wane aiki suka yi da dukiyar da muka damka musu amana a cikin tsawon shekaru? Wadanne dokoki suka yi domin ciyar da kasar nan gaba? Ina bilyoyin nairorin da ake dauna wa gwamnonin jihohinmu suke shiga; wajen raya kasa ko aljifan wadansu kalilan daga cikin al’umma? Me sanatocinmu ke yi a Abuja da tarin dukiyar da aka tanadar musu a matsayin albashi ko alawus? Me ’yan siyasarmu suka yi mana na a-zo-a-gani? Me jam’iyyun siyasar suka yi mana da za mu sake dora su bisa karagar mulki?
Wannan shi ne abin da ya dace da mu a halin yanzu, domin kuwa ba mai fitar da talaka daga cikin kangin da yake ciki face shi talakan da kansa, ba kuma wata hanya da ta dace mu bi domin kawo sauki, face mu rika yin tambayoyi, domin ta haka ne za mu samu amsar badakalar rayuwar da muke ciki. Allah Ya taimaka!