Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta bayyana cewa tsawaita wa’adin Babban Sifeton ’yan sandan kasar da ta yi da watanni uku bai ci karo da shari’a ba.
Sanarwar hakan ta fito ne daga bakin Lauyan Koli kuma Ministan Shari’a na Najeriya, Abubakar Malami SAN.
- COVID-19: Gwamnatin Kano ta raba takunkumi 10m kyauta
- Yadda ’yan bindiga suka kashe mijina wata daya da aurenmu
- Sheikh Abduljabbar ya maka Gwamnatin Kano a kotu
Cikin wata hira da Ministan ya yi da gidan Talabijin na Channels a ranar Laraba kan al’amuran da suka shafi siyasa, ya ce tsawaita wa’adin IGP Muhammadu Adamu da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi yana kan tafarki na tanadin da dokokin kasar suka yi.
Matakin da Shugaban Kasar ya dauka na tsawaita wa’adin Babban Sufeton zuwa watanni uku ya janyo ce-ce-ku-ce a yayin da lauyoyi da dama ke kalubalantar lamarin da cewa ya saba wa sashi na 215 da na 216 cikin kundin tsarin mulkin kasar da aka yi wa kwaskwarima a shekarar 1999 da kuma sashe na bakwai cikin dokar ’yan sandan Najeriya ta 2020.
Sai dai Ministan Shari’ar ya ce hujjar da lauyoyin suka dogara da ita ba ta yi daidai da hujjojin da Shugaban Kasar ya yi tsayuwar daka a kai ba.
A cewar Ministan, “Abin da nake fada a zahiri shi ne cewa a cikin tanadin bayanai na shari’a, da kuma hukuncin da Shugaban Kasar ya dauka na tsawaita wa’adin Babban Sufeton, an kiyaye dukkanin wasu ka’idodi da suka wajaba, kuma Shugaban Kasar ya yi hakan ne a cikin mahalli na doka,” in ji Malami.
A ranar Litinin ta makon jiya ce Babban Sufeton ’yan sandan wanda ya kama aiki daga ranar 4 ga watan Fabrairun 1986, ya kamata ya yi ritaya bayan da ya shafe shekaru 35 yana aikin kamar yadda tsarin aikin dan sanda a kasar ya tanadar.