Jam’iyyar APC mai mulkin Jihar Katsina ta yi alkawarin dorawa daga inda ta tsaya a fannin tsaro idan ta ci zaben gwamnan jihar da ke tafe.
Dan takarar gwamnan jihar a Jami’ar APC, Dikko Dikko Umar Radda, ne ya yi alkawarin a taron a Zauren Al’Umma na Katsina wanda kamfanin Media Trust tare da hadin gwiwar Cibiyar Cigaban Dimokuradiyya (CDD) da wasu kafafen yada labarai suka shirya.
- Ku ji tsoron Allah a alkawuranku —Lugga ga ’yan takarar gwamnan Kastina
- Gwamnan Yobe ya ba Gwarzuwar Musabaka ta Kasa kyautar gida
- A watan Maris za a fara hako man fetur a Jihar Nasarawa – NNPC
Dikko Radda, wanda abokin takararsa, Faouq Lawal Jobe, ya wakilta ya bayyana cewa su biyun suna da kwarewa, kasancewarsu malaman makaranta, ma’aikatan banki kuma wadanda suka taka rawa a gwamnatin mai ci daga shekarar 2015.
Ya ce zasu zasu maida hankali wajen inganta tsaro, ilmi da kuma kiwon lafiya da sauran fannonin rayuwa.