✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Tsaro: ’Yan Najeriya sun fara kare kansu da kansu —Monguno

Mashawarcin shugaban kasa kan sha'anin tsaro ya ce ’yan Najeriya sun gaji da mastalar tsaro da ke addabar kasar

Mai Bai Wa Shugaban Kasa Shawara Kan Sha’anin Tsaro (NSA), Manjo Janar Babagana Monguno mai ritaya, ya ce  ’yan Najeriya sun gaji da matsalar tsaro da ke addabar kasar, har sun fara tunanin daukar matakan kare kansu da kansu.

Monguno ya ce ‘mawuyacin hali’ da kasar ke ciki a halin yanzu na bukatar hadin kan masu ruwa da tsaki wajen ceto ta.

Ya bayyana wa manema labarai haka ne jim kadan bayan kammala taron Majalisar Tsaro ta Kasa wanda Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta ranar Laraba a Abuja.

Ana dai kallon kalaman na Monguno tamkar jirwaye mai kamar wanka  ne cewa ’yan Najeriya sun fara yanke kauna daga Gwamnatin Buhari game da sha’anin tsaro.

Mashawarcin shugaban kasar ya ce Shugaba Buhari na sane da damuwar ’yan kasa kan yadda matsalar tsaro ke ta kara kamari.

Ya bayyana cewa Majalisar na aiki wurjanjan kan sabbin dabarun da za su taimaka wajen dakile matsalolin tsaron da kasa ke fuskanta.

Daga nan ya ba da tabbacin za a samu sabon salon yaki da ta’addanci a kasar nan.

Monguno ya kuma bayyana cewa an kusa kammala bincike kan Harin Gidan Yarin Kuje domin hukunta wadanda sakacinsu ya yi sanadiyar aukuwar hakan.

A cewarsa, “Shugaban Kasa ne ya jagoranci taron a matsayin ci gaba da taron da aka soma makon jiya domin tattauna muhimman batutuwa da kuma nauyin da aka dora wa hukumomin tsaro.

“An kai wa jami’an tsaro hari kwanakin baya, wanda da an hada karfi da karfe wajen ba da bayanai da mun iya dakile harin.

“Amma wannan ba yana nufin nauyin kula da tsaro ya rataya ne a kan wadanda ba jami’an tsaro ba.

“Muna cikin mawuyacin hali, kuma Majalisar ta fahimci hakan. Shugaban Kasa ya fahimci damuwar ’yan kasa kan yadda matsalar tsaro ke ta kara dagulewa.

“Ina mai tabbatar muku babu wata dabarar da za mu yi wajen magance matsala har sai mun rungumi juna…,” inji Munguno.

Daga bisani, Munguno ya yi kira ga ’yan siyasar Najeriya da su lura da irin furucin da suke yi a cikin al’umma domin kauce wa haddasa tashin tashina.