Kwamitin Tsaro na Majalisar Wakilai, ya yanke shawarar ƙara Naira biliyan 50 da aka ware wa Ma’aikatar Tsaro a kasafin kuɗi na shekarar 2025 domin yaki da matsalar tsaro.
Shawarar ta biyo bayan ƙudiri da ɗan majalisa Philip Agbese, ya gabatar yayin zaman kare kasafin kuɗin ma’aikatar da Ministan Tsaro, Bello Matawalle, ya halarta.
- Jami’ar Jihar Gombe ta rantsar da sabbin likitoci 56
- Gwamnan Bauchi ya bai wa ɗalibai 4 da suka yi bajinta a JAMB kyautar N4m
Matawalle, ya bayyana cewa rashin wadataccen kasafi ya kawo cikas ga ayyukan sojoji, ciki har da samar da kayan aiki, gyara bariki, da kuma kula da jin daɗin jami’an tsaro.
Ya bayyana cewa adadin kuɗin da aka ware bai isa magance manyan matsaloli kamar sayen motocin yaƙi, biyan kuɗin inshorar ma’aikatan sojojin da suka rasu, da kuma inganta yanayin rayuwar jami’an tsaro.
Ya tabbatar wa ’yan majalisar cewa idan aka ƙara kuɗaɗen ma’aikatar, za a iya magance matsalar ’yan bindiga cikin watanni biyu.
Shugaban Kwamitin, Babajimi Benson, ya jaddada muhimmancin ɓangaren tsaro wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a ƙasa.
Ya kuma yaba da jajircewar sojoji duk da ƙarancin kuɗaɗen da suke fama da shi, inda ya bayyana cewa magance waɗannan matsaloli ya zama wajibi don tabbatar da tsaron ƙasa.