✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsarin tekunan duniya da abubuwan da ke cikinsu (3)

Nau’ukan Tsibiran Tekun Pacific Tsibiran da ke Tekun Pacific, wadanda adadinsu ya kai dubu ashirin da biyar (25,000), suna kunshe ne cikin bigirori uku da…

Nau’ukan Tsibiran Tekun Pacific

Tsibiran da ke Tekun Pacific, wadanda adadinsu ya kai dubu ashirin da biyar (25,000), suna kunshe ne cikin bigirori uku da ke ilahirin tsibirin. Bigiren farko shi ne bangaren Arewacin tekun, wanda ya kunshi tsibirai irin su tsibirin Mariana (Mariana Island), da tsibirin Caroline (Caroline Island), da tsibirin Marshall (Marshall Island), da kuma tsibirin Karbati (Karbati Island). Wadannan tsibirai su ne ke bigiren Micronesia, kuma gaba dayansu a dunkule ana kiransu “Micronesia Islands.” Kamar yadda bayani ya gabata a farko, wadanann tsibirai suna Arewacin tekun Pacific ne, arewa da Shacin Ekuator kenan.
Nau’ukan tsibirai na biyu su ne wadanda suke bangaren Kudu maso Yamma da shashen Ekuator. Shahararrun cikinsu su ne: tsibirin New Guinea, wanda shi ne tsibiri na biyu a girma a dukkan tsibiran da ke duniya. Tsibiri mafi girma a duniya shi ne tsibirin Greenland (Greenland Island). Sai tsibirin Bismarck (Bismiarck Island), da tsibirin Solomon (Solomon Island), da tsibirin Santa Cruz, da tsibirin banuatu, da tsibirin Fiji (Fiji Island), sai tsibiri na karshe, wato New Caledonia. Wadannan su ne tsibirin da ke bangaren Kudu maso Yammacin tekun Pacific, kuma a dunkule ana kiransu “Malanesia Islands.”
Sai bangare ko bigiren tekun Pacific na karshe, wanda shi ne bangare mafi girma daga cikin ukun – domin ya debo daga tsibirin Hawaii ne zuwa Nahiyar New Zealand. Wannan bangare shi ake kira: “Polynesia” ko “French Polynesia Islands.” Wannan bangare ya tattaro tsibirai irin su: tsibirin Tubalu (Tubalu Island), da tsibirin Tekelau (Tekelau Island), da tsibirin Samoa (Samaoa Island), da tsibirin Tonga (Tonga Island), da tsibirin Kemadec wanda ke yammacin tekun. Sauran tsibiran sun hada da: tsibirin Cook, da tsibirin Society, da tsibirin Austral (Austral Island), da tsibirin Markuessa, da Tuamotu, da Mangareba, da kuma Easter Island. Kamar yadda bayani ya gabata, wadannan tsibirai su ake kira: “French Polynesia Islands.”
Dangane da yanayin mahalli kuma, wadannan tsibirai da ke tekun Pacific sun kasu kashi hudu ne. ma’ana, yanayin tsarin wurin, na tudu ko gangara ko rashin kowannensu. bangaren farko su ake kira: “Continental Islands,” wato tsibiran da ke bakin gabar tekun kenan, wadanda suke makwabtaka da nahiyoyin duniya. Tsibiran da ke wannan bangare sun hada da tsibirin New Guinea (tsibiri na biyu a girma a duk fadin duniya kenan, bayan tsibirin Greenland), da tsibirin New Zealand (wanda shahararren tsibiri ne a duniyar yau), da kuma kasar Philipines. Duk tsibiran da ke makwabtaka da wadannan wurare su ake kira: “Continental Islands.”
Sai bangare na biyu ya kunshi tsibiran mahallinsu na kan tudu ne a inda suke, cikin tekun Pacific din. Wadannan su ake kira: “High Islands;” su ne tsibiran da ke kan tsunuka, ko ma dai gaba dayan mahallinsu tsauni ne, a tekun Pacific din. Su ne tsibiran da ke kan tsaunuka masu aman wuta, wato “bolcanic Islands.” Daga cikin wadannan tsibirai akwai tsibirin Bougainbille, da tsibirin Hawaii, da kuma tsibirin Solomon (Solomon Island).
bangare na uku su ake kira: “Coral Reefs Islands,” kuma su ne tsibiran da ke kan tsaunuka marasa bisa ko tsawo, wato gajerun tsaunuka kenan, kuma ba masu aman wuta ba. Wadannan tsaunuka da ke dauke da wadannan tsibirai asalinsu daga daskararren kunun aman tsaunuka ne, wato bolcanic Laba. Wanann shi ne kunun dutse mai zafi da ke malalowa daga saman tsauni a yayin da yake aman wuta. A yayin da wannan kunun dutse ke malalowa daga saman tsaunin, yana daskarewa ne nan take. Da zarar ya daskare sai ya zama tsauni mai matsakainin girma da tsawo, iya gwargwadon yawa da malalarsa. Wannan daskararren kunun dutse yana da fa’ida sosai. A bangaren farko yana zama taki ne ga shuke-shuken da ke wurin da ya malala. A bangare na biyu kuma, wani mahalli ne na sabuwar rayuwa. Allah buwayi gagara misali! Tsibiran da ke wannan mahalli su ake kira: “Coral Reefs Islands.”
Sai bangare na hudu kuma na karshe, wanda malaman kimiyyar teku ke kira: “Uplifted Coral Reefs Islands.” Wannan mahalli ya dara bangare na uku bisa da tudu, amma tsawonsa bai kai tsawon tsauni irin na al’ada ba. Tsibiran da ke wannan mahalli sun hada da: tsibirin Banaba (Banaba Island), da tsibirin Makatea (Makatea Island) da ke bangaren French Polynesia.
Wadannan su ne nau’ukan mahallan da ke dauke da tsibiran da ke Tekun Pacific.

Tashoshin Jiragen Ruwa
Abu ne sananne cewa duk wani teku da ke duniya yana da tashoshin jiragen ruwa da ke shawagi a cikinsa; dare da rana safe da yamma. Wadannan tashoshi dai suna bakin gabar kasashen da ke makwabtaka da tekun ne. A baya mun lissafo kasashen da ke makwabtaka da tekun Pacific, a wannan bangare, mai karatu zai san tashoshin da jiragen ruwa ke sauka da tashi daga gare su ne, a wannan babban teku na duniya.
Akwai tashoshin jiragen ruwa da ke sauka/tashi a tekun Pacific a kasashe daban-daban na duniya da ke makwabtaka da tekun. Tabbas akan samu tashoshin jiragen ruwa da ke shawagi a tekun Pacific sama da daya a wasu kasashen. A takaice dai, akwai tashoshin jiragen ruwa a: birnin Bangkok na kasar Tailand, da birnin Hong Kong na kasar Sin (China), da birnin Kao-Hsuing dake Lardin Taiwan. Wasu daga cikin tashoshin sun hada da: na birnin Los Angeles da ke kasar Amurka, da na birnin Manila da ke kasar Filifins, da na birnin Pusan da ke kasar Koriya ta Kudu, da na biranen San Francisco da Seattle da ke kasar Amurka. Daga ciki har wa yau akwai tashar birnin Shanghai da ke kasar Sin (China), da na birnin Singapore da ke kasar Singafo, sai na birnin Sydney da ke kasar Ostiraliya. Sauran su ne na birnin bladibostok da ke kasar Rasha, da wanda ke birnin Wellington na kasar New Zealand, sai na karshe, wanda ke birnin Yokohama na kasar Jafan.
Wadannan, a takaice, su ne tashoshin jiragen ruwan da ke shawagi a cikin tekun Pacific, dare da rana safe da yamma.

Yanayin Ruwa
Tekun Pacific na dauke da ruwan da babu wani teku a duniya mai dauke da irinsa, wajen yawa, da zurfi, da kuma fadi. Tekun Pacific ne ke dauke da kashi 50 cikin 100 na ruwan da ke duniya baki daya; tsakanin ruwan zartsi (gishiri) da ruwan gardi. Idan ka raba ruwan duniya baki daya, rabin adadinsa daga tekun Pacific ne. A ma’aunin “Cubic,” adadin ruwan tekun Pacific ya kai miliyan 714 (714 million cubic meter). Ruwan tekun Pacific na dauke da yanayi nau’uka uku ne; da na sanyi, da na dumi, sai na kankara. Wadannan nau’ukan yanayi suna sauyawa ne iya gwargwadon yanayin iska da ke bugawa ko shawagi a fadin wannan duniya tamu.
A iya binciken malaman kimiyyar teku, dandanon ruwan tekun Pacific ba daya yake ba. Na’am, yana da dandanon gishiri tabbas, amma bangaren tekun da ke can kusa da sashen Ekuator, makuran arewaci inda tekun ya fara, ya fi dandanon gishiri fiye da kowane bangarensa. Sannan wannan bangaren ne ya fi tsananin sanyi inda har yakan kai mizanin sandarewa (Freezing Point) a wasu lokuta na shekara.