✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsarin Gadon Kamanni A Kimiyyance

Me ya sa idan aka haifi xa namiji ya fi kama da mahaifiya, ita kuma mace ta fi kama da mahaifinta, saboda wai halittar namiji…

Me ya sa idan aka haifi xa namiji ya fi kama da mahaifiya, ita kuma mace ta fi kama da mahaifinta, saboda wai halittar namiji ta fi yawa a jikin mahaifiya, haka ma mace ta fi yawa a jikin mahaifi? Ko hakan gaskiya ne?

Daga Hassana I., Birnin Kudu

Amsa: A’a zancen ba haka yake ba a tsarin gadon kamanni na kimiyya. Kuma ke ma kanki idan kika lura sosai a cikin dangi abin ba haka yake ba. Domin tabbas a cikin danginki za ki samu ‘ya da ba ta yi kama da mahaifinta ba sam-sam, sai dai mahaifiyarta, ko kuma yaron da bai yi kama da mahaifiyarsa ba sai dai mahaifinsa. Don haka kenan wannan shaci-faxi ne kawai.

A tsarin gado akwai wasu yanayin halittar jiki da suka fi wasu qarfi, misali a xauki tsayi da gajarta. A tsarin gado tsayi ya fi gajarta qarfi, don haka idan mace mai tsayi ta haifi ‘ya’ya huxu da gajeren mutum, akan ga uku cikinsu dogaye, xaya gajere, ko biyu dogaye, xaya matsakaici, xaya gajere, amma da wuya a ga ‘ya‘ya gajeru sai dai duk idan iyayen biyu gajeru ne.

Haka nan ma kamannin fuska ko yanayin fuska, wani ya fi wani qarfin ‘ya’yan halitta na kamanni. Mahaifiya mai qarfin qwayoyin kamanni za a ga ‘ya’yanta kusan duk ita suka biyo, xaya ko biyu ne suka bi kamannin mahaifi. Haka ma idan mahaifin shi ne mai qarfin qwayoyin halittu na gadon kamanni.

To haka tsarin gado yake, siffar da ta fi qarfi a wajen gado, a jikin ko wane ne, matar ce ko mijin, ita ce za ta rinjayi maras qarfi a ‘ya’yansu. A haka ma akan yi gadon wasu cutuka, wanda aka tava bayaninsa a baya a wannan shafi.

Wai ko akwai wani sinadari ne da ya haxa gujya da gyaxa?

Daga S. Umar Malumfashi

Amsa: Lallai Mallam Umar gyaxar ce ta shige ka ko kuwa gujyar? Da fatan ka noma ko da xaya daga cikinsu bana. Ai idan ka lura gujiya ta ma fi kama da wake ba gyaxa ba, domin idonsu da xanxanonsu kusan iri xaya ne. Amma dai duka ukun abinci ne na ayari xaya tunda a cikin qasa ‘ya’yansu ke fitowa, wato legumes a kimiyance, kuma duka suna da sinadarin mai gina jiki wato protein, wanda shi ne sinadarin abinci da ya fi yawa a cikin dukansu.

Ko ana iya warkewa daga qyasbi gaba xaya? Domin sai ya tafi sai a ga ya dawo.

Daga Nasiru Kainuwa Haxejia

Amsa: Da yake qyasbin a likitance iri biyu ne; wanda qwayoyin cuta ke kawowa da wanda borin jini ko borin fata ke kawowa. Wanda qwayoyin cuta ke kawo shi ya fi saurin tafiya idan aka ba da magungunan da suka dace, amma na borin jini yana da wahalar sha’ani domin kamar akwai abubuwa a wurin zaman mutum, kamar bushewar yanayi a lokacin rani, zai iya kawo wa wasu matsalar. Don haka ne za ka ga wasu da damina abin ya tafi amma da rani ya dawo, saboda a yanayin gari ne ba a wani abu ba.

Shin idan majina ta yi qaranci a jikin mutum zai iya fuskantar matsala? Me ya sa idan mutum ya ci yaji sai ya riqa zubar da majina?

Daga Garba Sabiyola, Gashuwa

Amsa: Ai a likitance ma har yanzu ban zo karatun inda aka ce ga wani da jikinsa ba ya iya sarrafawa da fitar da majina ba, ballantana ta yi qaranci, sai dai ma akasin haka, wato akwai ciwon yawan majina mai suna cystic fibrosis. 

Don haka da wuya dai ka ji an ce ga wani shi kwata-kwata jikinsa ba ya iya samar da majina. Hasali ma muna ganin idan aka haifi jaririn da jikinsa ba ya iya samar da majina to nan da nan zai iya cikawa, saboda ko abinci a cikin hanji sai fa hanji ya saki majina ake narkashi, ka ga kuwa wanda ke da qaranci ko rashin majina a jiki ai ba zai iya rayuwa. Wato dole mutum ya yi la’akari da cewa majina ba a baki da hanci kaxai take ba, akwai ta a ciki akwai ta a qirji.

Game da vangaren tambayarka na biyu a ilimin magunguna an san cewa yaji yana sa danqararriyar majina ta narke ta zama ruwa, shi ya sa wasu masu magungunan sukan ce a riqa cin yaji idan majina ta danqare a hanci ko qirji an kasa fito da ita ta hanyar tari. Wannan ne ma kan sa wasu yin gudawa idan suka ci yaji saboda majinar ciki na tsinkewa, sai hanjin ma ya saki a yi ta zawo.

Me ke sa a riqa yin gyatsa? Shin gyatsa ciwo ne?

Daga Haruna Muhammad, Katsina

Amsa: Gyatsa ba ciwo ba ne, amma za ta iya zama alama mai nuni da wani ciwo a ciki idan aka fiya yinta. Yau da kullum idan muka ci abinci muka sha ruwa, bayan ‘yan xaqiqu zuwa mintoci mu kan saki gyatsa, wadda take a matsayin iskar da muka haxiye a abinci da ruwa. Amma idan aka samu wani shi a ko da yaushe gyatsa yake ko ya ci abinci ko bai ci ba, to tabbas wannan akwai alamun matsala sai ya ga likita an duba shi.

Ni na xan manyanta domin shekaruna sun haura 60 kuma ina fama da ciwon gwiwoyi, shi ne nake neman shawarar abinda zan riqa ci.

Daga 

Amsa: To Hajiya Zuwaira ai kin san jikin tsufa dama sai a hankali. Mata da dama bayan shekaru 50 sukan yi fama da wani ciwo na zaizayewar qashi saboda sinadarin dake taimaka muku qara musu lafiyar qashi a quruciya yake da yawa, da an tsufa yake vacewa. Don haka ya kamata a samu a duba gwiwoyin a gani ko zaizaiyewar ce, ko kuma a’a sanyin qashi ne ko kuma wani abu daban.

Duk da haka dai za ki iya qara yawan shan madara da cikwi, wato cheese a abincinki domin su suka fi komai sinadarin calcium mai qara qwarin qashi. Da fatan za a samu a je a duba lafiya qafar.