✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsarin amfani da waya nau’in Blackberry (3)

Wayoyin salula masu dauke da masarrafar Imel irin na Blackberry dai su ne: AT&T Tilt, da HTC Adbantage d7500, da HTC TyTN, da Motorola MPd220,…

Nau’in wayar BlackberryWayoyin salula masu dauke da masarrafar Imel irin na Blackberry dai su ne: AT&T Tilt, da HTC Adbantage d7500, da HTC TyTN, da Motorola MPd220, da Nokia 6810, da 6820, da 9300, da 9300i, da kuma 9500.  Cikin jerin wayoyin har wa yau akwai dukkan ayarin wayoyin Nokia zubin E-series (ban da E71 da E66), sai kuma ktek 9100, da ktek 9000, da Samsung E719, da Siemens SK65, da SonyEricsson P910, da P99, da M600i, da kuma P1.  Wadannan, a halin yanzu, su ne nau’ukan wayoyin salula masu dauke da masarrafar Imel na wayar Blackberry, watau Blackberry Email Client.  Ba mu san abin da gobe zai haifar ba.

Tasirin Amfani da Blackberry a Duniya
Ko shakka babu amfani da wayar salula nau’in Blackberry yana tasiri sosai wajen aiwatar da sadarwa a yanayi kayatacce kuma mai gamsarwa.  Musamman ganin cewa kamfanoni da hukumomi da daidaikun mutane sun rajja’a wajen amfani da wannan waya.  Dalilan hakan dai ba nesa suke ba. Da farko, bayan yawaitan hanyoyi da manhajoji ko masarrafan sadarwa da wayar ke dauke da su, akwai kuma ingancin tsaro wajen sadarwa, wanda shi ne abin da galibin kamfanoni ke bukata.  A tsarin aikawa da sakonni ta Blackberry, da zarar ka rubuta sako ka aika, nan take za a narkar da sakon don kariya, har sai ya isa inda aka aike shi.  Wannan ta sa wasu kasashe a Gabas ta Tsakiya suka fara damuwa da wannan tsari na boyewa tare da narkar da bayanai ta yadda babu na’ura mai iya hangowa balle ta karance su yadda za a fahimci sakon da ke cikinsu.  Daga sakon tes, zuwa Imel, har rubutattun sakonnin hira da na murya, duk narkar da su ake yi har sai sun isa inda aka aike su.  
Wani abin da ya kara wa wannan tsari wuyan sha’ani ga hukumomi masu son tace bayanai na murya ko rubutattu da ake aikawa a tsakanin kayayyakin sadarwa kuma shi ne, dukkan sakonnin da ake aikawa sai sun dire a Uwar Garken kamfanin da ya kera wayar a can kasar Kanada, sannan su isa muhallin da ake jiran isar su.  Shi ya sa a ranar 1 ga watan Agusta kasar Hadaddiyar Daular Larabawa (United Arab Emirates) ta toshe kafar amfani da tsarin Intanet da Imel da rubutattun hira ta hanyar wayar Blackberry, saboda dalilai na tsaro.  A kasar hukuma ta saba tace ire-iren wadannan bayanai daga wayoyin salular da ake amfani da su, don tsaron lafiyar jama’a da ma baki da ke shigi-da-fici a kasar a kullum.  To amma saboda tsananin tsaro da wannan waya ta Blackberry ta sifatu da shi, sun kasa samun isa ga ire-iren wadannan bayanai da mutane ke aikawa ta wannan waya.  Don haka suka toshe dukkan kafar Intanet da duk wani mai Blackberry zai iya bi ya aika da sako.  A halin yanzu idan kana Dubai, sai dai ka kira, ko ka yi tes, amma batun Imel da Intanet kam sai dai ka hakura.  Hukuma ta ce muddin kamfanin bai yi wani hobbasa ba wajen ganin ya warware wannan matsala kafin 11 ga watan Oktoba, to za ta toshe hanyar amfani da wayar ma gaba daya.  A halin yanzu akwai wayar salula nau’in Blackberry guda 500,000 da ake amfani da su a kasar.
A kasar Saudiyya ma hukuma ta koka da wannan tsari na mu’amala da wayar Blackberry.  Don haka ita ma, daidai lokacin da ake wancan dambarwa a Hadaddiyar Daular Larabawa, ta yi barazanar cewa za ta toshe kafar sadarwar Intanet ga duk mai wannan waya, muddin kamfanin Research in Motion bai yi wani abu ba wajen ganin hukuma ta samu kai wa ga ire-iren bayanan da take so ko ake aikawa.  Ai nan take sai kamfanin ya fara shirye-shiryen ganin ya amsa wannan kira.  Domin akwai wayoyin Blackberry wajen 700,000 da ake amfani da su a kasar.  Ya zuwa yanzu, kamfanin ya fara tattaunawa da hukumar Saudiyya, inda ya yi tayin sanya wata Uwar Garke (Network Serber) da dukkan sakonnin da masu wayar ke aikawa za su rika bi, gwamnati na tace su, kafin su zarce zuwa ga wadanda aka aika musu su, a kasar suke ko a wajen kasar. Domin kasar Saudiyya da ma galibin kasashen Larabawa duk suna tace tsarin sadarwa da ake gudanarwa ta hanyoyin kayayyakin sadarwa irinsu kwamfuta da wayoyin salula da sauransu.  Bayan kasar Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa da Indonesiya da Bahrain da Indiya da Aljeriya da kuma kasar Lebanon, duk sun fara tayar da kura kan wannan tsari na rashin iya tace bayanan da wannan waya ta Blackberry ke aikawa, kuma akwai hasashen cewa su ma suna iya cewa sai an musu irin abin da ake son yi wa Saudiyya, in kuwa ba haka ba, to duk wani mai wayar Blackberry ya jefar da ita a bola.

Mun kammala