✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsarin amfani da waya nau’in Blackberry (2)

Tsarin Amfani da Wayar Blackberry Ana iya amfani da wayar Blackberry ta hanyoyi uku.  Hanyar farko ita ce, ka sayi wayar a kasuwa, ka sanya…

Nau’in wayar BlackberryTsarin Amfani da Wayar Blackberry

Ana iya amfani da wayar Blackberry ta hanyoyi uku.  Hanyar farko ita ce, ka sayi wayar a kasuwa, ka sanya katin SIM dinka a ciki, sai kawai ka ci gaba da amfani da ita kamar sauran wayoyi.   A wannan tsari, za ka iya yin kira, kuma a kira ka; ka yi tes, kuma a aiko maka.  A takaice dai, za ka rika amfani da tsarin sadarwar kamfanin da ka sanya katinsu.  Amma ba za ka iya amfana da galibin masarrafai da manhajojin da wayar ke dauke da su ba.  Hanya ta biyu kuma kana iya saya, ko ka je daya daga cikin kamfanonin waya da muke da su a Nijeriya ka saya (kowanne cikin kamfanonin waya da muke da su a kasar nan suna sayar da wannan waya), sannan ka bukaci su farkar maka da ita, watau Actibation kenan.  Kowace waya nau’in Blackberry na zuwa ne da kalmomin izinin shiga (Pin Cord) guda takwas, kuma da su ake amfani wajen gabatar da abubuwa da dama a wayar.  Kamfanin zai bukaci wadannan kalmomi a gidan yanar sadarwarsa, ko kuma a lokacin da kaje, don su shigar da wayarka cikin babbar manhajar sadarwarsu, kafin ka fara amfana da tsarin Intanet da na Imel da wayar ke dauke da su. Wannan tsari na biyu shi ake kira Blackberry Internet Serbice (BIS).  Kamfanonin wayar kasar nan na da wannan tsari, kuma idan ka shiga, a kullum za ka iya mu’amala da fasahar Intanet a wayar, da manhajar Imel, da kuma hanyar hirar ga-ni-ga-ka.  Duk lokacin da ka samu sako a akwatin Imel dinka, nan take wayar za ta sanar da kai cewa sakon Imel ya shigo; kamar dai yadda wayarka ke sanar da kai idan ka samu sakon tes.  Sai dai kuma, dangane da tsarin biya da ke tsakaninka da kamfanin, duk wata za ka rika biyan kudin hanya, ko dai kafin wata ya kama, ko kuma bayan ya kare.  In kuwa ba haka ba, to ba ka da sabis.
Sai tsari na uku, wanda kamfanoni ne ke amfani da shi, kuma ya kunshi jona wayar da wata manhaja ta musamman mai suna Blackberry Enterprise Serber (watau BES).  Wannan manhaja za a sanya ta ne cikin kwamfuta ta musamman a ofishin kamfanin, sannan a hada ta da tauraron dan Adam, wanda zai rika aiwatar da sadarwa ta wayar iska tsakaninsa da dukkan ma’aikacin kamfanin da ke dauke da wayar, da Cibiyar Bayanai (Network Operations Center – NOC) da ke kamfanin Research in Motion a can kasar Kanada, da kuma kamfanin sadarwar da wayoyin ke amfani da katin SIM dinsa. Wannan tsari yana da tsada sosai, amma ba abin da ya fi shi kayatarwa wajen sadarwa.  Shi ma, kamar tsarin da ya gabace shi, dukkan kamfanonin sadarwar wayar salula da ke kasar nan na iya aiwatar da shi.  Bari mu dan kara bayani kan yadda wannan tsari na BES ke gudana.
Mu kaddara Malam Jatau na da kamfani mai dauke da ma’aikata 30, kuma yana son a dukkan lokuta kowane ma’aikaci na bakin aikinsa; a gida yake, ko ofis, a gari yake, ko a halin tafiya. Sai ya je kamfanin MTN misali (kamfanin Zain da Etisalat da Glo ku yi hakuri, misali nake bayarwa) ya bukaci wannan tsari.  Kamfanin MTN zai baiwa kowane ma’aikaci wayar Blackberry ne guda daya, mai dauke da katin SIM din kamfanin, wanda kuma aka jona shi da babbar cibiyar sadarwar kamfanin. Sannan sai ya je inda ofishin kamfanin Malam Jatau yake, don sanya wannan manhaja ta Blackberry Enterprise Serber a Uwar Garken (Network Serber) da ke ofishin.  Sannan ya jona dukkan na’urorin da za su hada alaka a tsakanin babbar cibiyar sadarwarsa ta waya, da wayyoin salular da ya baiwa wadancan ma’aikata, da kuma babbar cibiyar taskance bayanai ta kamfanin Research in Motion da ke can kasar Kanada.  Da zarar ya yi haka, an gama komai.  Da wannan tsari, kowanne cikin ma’aikatan nan zai iya aiko sakon Imel cikin gaggawa zuwa ofis, don sanar da ofis halin da yake ciki kan aikin da aka tura shi.  Haka za a iya aika masa da sakon Imel ta gaggawa.  Haka za a iya hira da shi a tsarin hirar ga-ni-ga-ka, watau Instant Messenger.  Idan kamfanin ya bayar da lambar wayarsa ne ga masu hulda da kamfanin, to duk sa’adda suka aiko sakon tes, ko na Imel, kai tsaye zai wuce zuwa wayarsa, inda wayar za ta sanar da shi cewa sako ya iso.  Idan yana bukatar karantawa, ba ya bukatar sai ya bude wayar; akwai alamar da aka tanada masa a jikin wayar wacce zai matsa, sai kawai sakon ya budo.  
Dukkan sakonnin bayanai – irinsu tes, da Imel, da rubutattun sakonnin hirar ga-ni-ga-ka – suna bin hanyoyi uku ne ko hudu, kafin su isa inda aka aike su, a wannan tsari na BES.  Idan aka aika wa wani ma’aikaci sakon Imel misali, sakon za ta zarce ne kai tsaye zuwa cikin wannan babbar manhaja ta BES da ke kamfanin, wacce a dakace take tana jiran sakonni masu shigowa.  Da zarar ta kalli sakon da ya shigo, sai ta cilla wa wancan babbar cibiyar bayanai na kamfanin Research in Motion da ke kasar Kanada. Wancan cibiya da ke kasar Kanada kuma sai ta cilla wa cibiyar sadarwar kamfanin MTN, wacce mai’aikacin ke dauke da katin SIM din kamfaninta.  Da zarar sakon ya iso kamfanin MTN, sai ita kuma ta aika wa ma’aikacin cikin wayarsa.  Duk wannan zai faru ne cikin kankanen lokaci, sanadiyyar tasirin kayayyaki da hanyoyin sadarwa ta wayar iska.  Sakon na shigowa wayar za ta sanar da shi nan take. Wannan shi ne yadda ake gudanar da sadarwa a tsakanin manhajar BES da kuma wayar Blackberry.

Zubin Wayoyin Blackberry
Akwai wayoyin Blackberry da dama da aka kera su a yanayi da kintsi daban-daban.  Kashin farko su ne wadanda aka kera cikin shekarar 1999, wadanda kuma galibinsu  duk ba su da wasu launukan da suka wuce fari da baki (watau monochrome, ko kuma black and white).  Daga shekarar 2006 zuwa 2008 sai kamfanin ya samar da zubin da ya yi wa lakabi da Blackberry Pearls.  Kafin shekarar 2008 ta kare, sai kamfanin ya samar da wasu zubin masu suna Blackberry Curbe, kuma irinsu ya yi ta kerawa har sai da shekarar 2009 ta kare.  A karshen shekarar kuma sai ya kirkiri zubin Blackberry Storm, wadanda ya yi ta kerawa har cikin shekarar 2010.  Daga farkon shekarar 2010 kuma zuwa tsakiyar shekarar, kamfanin Research in Motion ya sake kera wasu nau’uka da sake sanya musu sunan Blackberry pearls, da Blackberry Curbe.  Dukkan wadannan zube-zube na nau’in Blackberry suna dauke ne da adadin 7000, da 8000, da kuma 9000 series, kamar yadda ake kiransu a jumlace.  Wayar Blackberry ta baya-bayan nan da kamfanin ya kera ita ce nau’in Blackberry 9300.  

Wayoyin Salula Masu Kama da Blackberry
Akwai wasu cikin wayoyin salula na zamani da aka kera su dauke da masarrafar Imel ta musamman da wayar Blackberry ke dauke da ita, watau Blackberry Email Client.  Wannan ke sa su sifatu da wata dabi’a ko yanayi irin na Blackberry, to amma fa, kama da wane ba ya wane, ko kadan.  Zan so mai karatu ya samu sunayensu, domin idan mun kasa mallakar wayar Blackberry, to mu san cewa akwai wasu nau’uka da za mu iya mallaka don huce fushin rashinta.  Tabbas Blackberry waya ce abin alfahari da morewa, to amma Allah Bai yi yatsun hannayenmu iri daya ba, balle zanen da ke tafukan hannunmu su dace.
Za mu cigaba