✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsari da yadda na’urar “Black Bod” ke aiki a jiragen sama (4)

A karshe dai Allah Ya yi, an gano inda jirgin Air Asia mai lamba QZ8501 ya fada; can karkashin tekun Jaba na kasar Indonisiya. Wato…

A karshe dai Allah Ya yi, an gano inda jirgin Air Asia mai lamba QZ8501 ya fada; can karkashin tekun Jaba na kasar Indonisiya. Wato bai ma riga ya shiga Singafo ba. A halin yanzu, kamar yadda masu karatu sun ji a labarai, ana can ana ta ceto gawarwakin fasinjoji da matuka jirgin. Ba wannan kadai ba, hatta na’urar “Black Bod” dake jirgin an samo su; duk guda biyun, kamar yadda mai karatu zai gani a hoton dake shafin. Muna rokon Allah Ya gafarta wa musulmin cikinsu, ya kuma sa mu cika da imani, amin. Kada a mance dai, ba mu gushe ba muna bayani ne kan asali da samuwar wannan na’ura. A wannan mako bayani muka kawo kan yadda aka yi jama’a a duniya galibi suke kiran wannan na’ura da suna: “Black Bod,” maimakon “Flight Data Recorder” kamar yadda yake rubuce a jikinsa.

Asalin Sunan “Black Bod”
Kamar yadda bayani ya gabata a kasidar farko, kalmar “Black Bod” da ake ishara da ita don nufin na’urar “Flight Data Recorder,” ba asalin sunan na’urar ba kenan. Suna ne da wasu ko wani ya kirkira, don nufin wannan na’ura, ta la’akari da irin aikin da take yi, da rashin tabbas na yadda take aiwatar da aikin nata, a zahirin fahimta irin ta dan adam. Har yanzu dai ba a san wanda ya sanya wa wannan na’ura wannan suna ba. Don haka ne ma, zai yi wahala ka ji a ilimance, wani masani ko wani marubuci, a cikin littafi na ilimi, ya ambaci wannan na’ura da kalmar “Black Bod” kadai yayi shiru.
To, shin, asalin launin wannan na’ura baki ne, da har ake kiranta da “Black Bod”? Ko kadan! Launin wannan na’ura ja ne, ko ince launin ruwan lemo (Orange Color). Idan ka ga wannan na’ura da launi baki, to ba hakikanin na’urar ba ce. Sai dai a cikin fim. Amma a zahiri launin na’urar ya sha bamban da sunan da ake ambatanta da shi. Wannan ne ma ke nuna cewa lallai wannan suna na “Black Bod” suna ne na kan titi (Unofficial Name), ba hakikanin sunan da masu kera ta suka sa mata ba ne (Official Name). To ta ina ta samo wannan suna?

ka’idar Kimiyyar kere-kere
Abu na farko da malaman tarihin wannan na’ura suka fara dubawa, wanda kuma yana iya zama dalilin da ya sa wasu ke kiran wannan na’ura da “Black Bod,” shi ne wata ka’idar kimiyyar kere-kere da ta shahara a fannin kera jiragen sama. Wannan ka’ida ta kimiyya, wadda tana daya daga cikin ka’idojin ilimi da suka taimaka wajen samar da jirgin sama da yadda yake aiki, tana bayani ne kan sarkakiyar dake cikin tsarin aikinsa. Ga abin da wannan ka’ida take cewa:
“An tsara kirar jirgin sama ne a yanayi mai sarkakiyar fahimta; fahimtar dabi’unsa da yadda yake aiki na yiwuwa ne kadai ta la’akari da irin bayanan da (matukinsa) ke shigar masa (kafin ya tashi), da irin bayanan da yake fitarwa (na yanayin gudu, da nisa daga kasa, da sauransu) a halin tafiya a sararin samaniya.”
Abin da wannan ka’ida ke nunawa shi ne, sanin “hakikanin” yadda jirgin sama ke aiki; daga tashi zuwa shawagi har sauka, abu ne mai ban al’ajabi, wanda fahimtar hakikaninsa ba ya yiwuwa ta hanyar kallo irin na ido. Bayan bayanan da ake ganin matuki na baiwa jirgi, da irin yadda jirgin ke amsawa sanadiyyar bin umarnin, wadanda abubuwa ne da ake iya gani a zahiri, bayan su, sai dai a sa ido kawai. Domin ba abu ba ne da za a iya bayaninsa har wani ya fahimta, saboda tsauri da sarkakiyar da ke cikinsa.
Wannan ka’ida da ke sama na nuna cewa dukkan na’urori da ake iya sarrafa su don aiwatar da wani aiki na musamman, hakan na faruwa ne ta matakai guda uku. Na farko shi ne “abin da ake shigar wa na’urar.” Wannan shi ake kira “Input.” Sai mataki na biyu, wato abin da “na’urar ke bayyanawa” bayan an shigar mata. Wannan shi ake kira “Output.” Sai mataki na karshe (wanda shi ne na biyu a zahiri), wato “yadda na’urar take sarrafa abin da aka shigar mata, kafin ta bayyana sakamakonsa. Wannan shi ake kira “Processing.” To amma idan muka kalli jirgi sai mu ga matakin farko da na biyu ne kadai muke iya gani, a zahiri. Dayan matakin, wato sarrafa umarni, ba wanda zai ce maka ga “hakikanin” abin da ke wakana a cikin inji ko na’urorin jirgin.
A zamantakewa ta rayuwar Bature, duk wani abu mai siffa irin wannan, yakan kira shi da suna: “Black Bod.” Wato, kai dai a ci baure, amma ban da tona cikinsa. Ba kuma jirgin sama kadai ba, duk wata na’ura da muke amfani da ita – irin su Talabijin, da Rediyo, da Kwamfuta, da Wayar Salula, da Fanka, da Firji, da sauran makamantansu – haka suke; hada har da na’urar “Taskance bayanai na jirgin sama” – Flight Data Recorder.
Da wannan ne wasu suka ce, ta yiwu an yi la’akari da wannan ka’ida ta kere-kere ce aka sanya wa wannan na’ura suna: “Black Bod.” Kenan, idan aka ce: “Black Bod,” an yi la’akari da ka’idar tunanin da ya samar da na’urar kenan. Amma fa kada a mance, ba asalin sunan wannan na’ura ba kenan.
Fina-finan Zamanin Da
Wasu malaman tarihi kuma suka ce a a, asalin wadanda suka kirkiri kalmar “Black Bod” don ishara ga wannan na’urar su ne masu shirya fina-finai, musamman na zamanin baya. A cikin fina-finan da suka yi fice a baya, an samu inda jirage suka yi hatsari, kuma aka samu daman ceto wannan na’ura, wadda a cikin fina-finan ake nuna cikin na’urar mai launi baki, kuma suna rika kiranta da suna: “Black Bod.” Shi ya sa wasu malaman tarihi ke ganin asalin masu shirya fina-finai na zamanin baya ne suka fara kiran wannan na’ura da wannan suna na bayan fage. Wasu kuma suka ce a a. Ba inda wannan suna ya samo asali ba kenan.

Hira da Injiniya Warren
Wasu malaman tarihi suka ce sunan ya samu ne a lokacin da wani dan jarida ke hira da Injiniya Warren, daya daga cikin wadanda suka kirkiri wannan na’ura, kamar yadda bayani ya gabata a kasidar farko. Bayan dan jaridar ya ji bayanai kan yadda Warren ya kirkiri na’urar, da yadda na’urar take gudanar da aikinta, da dai sauransu, cikin mamaki da jin dadi, sai ya ce: “This is a wonderful Black Bod!” (Kai, wannan wata irin na’ura ce mai ban mamaki da cike da al’ajabi). Wannan, a cewar wasu malaman, shi ne dalilin samuwar wannan suna, musamman ganin cewa wanda ya fadi kalmar dan jarida ne. Babu mamaki daga nan ma ya ci gaba da ambaton na’urar da wannan suna. Wasu malaman kuma suka ce a’a.

Daga Injiniya Newton
A karshe, wasu malaman tarihi sun alakanta wannan kalma ga Injiniya E. Newton, daga cikin injiniyoyi masu hazaka da suka taimaka wajen samar da na’uar. Tarihi ya hakaito wannan Injiniya, a shekarar 1958, yana ambaton wannan na’ura da kalmar Black Bod, musamman cikin wani bincike na musamman ko rahoto da ya rubuta. Wasu suka ce wannan shi ne dalili mafi karfi daga cikin sauran dalilan da suka sa ake kiran wannan na’ura da kalmar: “Black Bod,” saboda samuwar kalmar daga bakin daya daga cikin wadanda suka taimaka wajen samar da ita.
Ko ma dai mene ne, ana so ko ba a so, wannan na’ura ta fi shahara da suna: “Black Bod” a duniya, fiye da asalin da sunan da aka ba ta ko ake ambatonta da shi a tsakanin masana. Suna ne na kan titi. Kuma, ga dukkan alamu, jama’a sun fi samun saukin ambaton wannan suna da sunan: “Flight Data Recorder.”