✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsare Musulmi ’yan Uighur da China ke yi babban laifi ne —MDD

Ana zargin China da yi wa Musulmi ’yan kabilar Uighur kisan kare dangi

Ofishin Hukumar Kula da Kare Hakkin dan Adam na Majlisar Dinkin Duniya ya bayyana cigaba da tsare Musulmi ’yan kabilar Uighurs da gwamnatin China ke yi a matsayin cin mutunci bil adama ne. 

Ofishin ya ce tsare Musulman da China ke yi ka iya zama babban laifi da take hakkin bil Adama, yayin da sauran kasashen duniya suka kira lamarin da “Kisan Kare Dangi.”

Hukumar ta fadi haka ne sakamakon wallafa wani rahoto da shugabanta Michelle Bechelet ya jagoranta, ya kuma gabatar daf da cikar wa’adinsa na aiki a cewar kafar yada labarai ta Aljazeera.

Rahoton mai shafuka 45 ya ya yi kira ga gwamnatin China da ta saki duk [’yan kabilar Uighurs tsirari] wadanda take tsare da su ba tare da wani sharadi ba, kuma nan take.

Sannan ta bayyana wa iyalan sauran wadanda suka bace inda ’yan uwansu suke, ta kuma sake nazarin dokokinta na cikin gida na tsaro, tare da soke dukkan dokokinta na wariyar al’umma.

Wannan ba shi ne karon farko da kasar China take shan suka a kan yadda take musguna wa ’yan kabilar Uighur da ke Arewa maso Yammacin yankin Xinjiang na kasar kasncewar yawancinsu Musulmai ne.

Rahoton wani kwamitin kawar da wariyar launin fata na MDD da aka wallafa shekara hudu da suka wuce, ya bayyana cewa, hukumomin China na tsare da mutane sama da miliyan daya a kasar, a wasu cibiyoyi daban-daban a yankin Xinjiang.

Gwamnatocin Amurka da Britaniya da Canada da Faransa, tuni suka ayyana yadda gwamnatin Chaina ke yi wa ’yan kabilar Uighurs a matsayin “Kisan kare dangin”.