✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsananin sanyi ya kashe mutum 70 da shanu 70,000 a Afghanistan

Akalla mutum 70 da shanu 70,000 sun mutu sakamakon tsananin sanyi a kasar.

Akalla mutum 70 da shanu 70,000 ne suka mutu cikin mako daya sakamakon tsananin sanyi a wasu sassan Afghanistan.

Ma’aikatar Kula da Iftila’i ta kasar ta tabbatar wa kafar Al-Jazeera da aukuwar hakan ranar Laraba.

Rahotanni sun ce cikin makonni biyun da suka gabata, sassan kasar da dama na fama da yanayi na sanyi mai tsanani, wanda karfinsa a tsakiyar kasar ya sauko zuwa matakin -33C (-27F) a karshen mako.

“Nesa ba kusa ba, wannan shi ne sanyi mafi tsanani da aka fuskanta a shekarun baya-bayan nan.

“Muna sa ran sanyin ya ci gaba nan da mako ko fiye da haka,” in ji Mohammad Nasim Muradi, jami’i a Ofishin Hasashen Yanayi na kasar.

Mai magana da yawun Masarautar Musulunci na Afghanistan, Zabihullah Mujahid, ya mika ta’aziyya a madadin gwamnati ga ‘yan uwan wadanda sanyin ya kashe.

Bayyanai sun ce wannan shi ne sanyi mafi muni na biyu da Afghanistan ta fuskanta tun bayan da Taliban ta karbe ragamar mulkin kasar a Agusta, 2021.