Kocin Manchester City Manuel Pellegrini ya nuna bacin ransa a kan yadda alkalin wasa Jonas Eriksson dan asalin Swidin (Sweden) ya hura wasa a tsakanin kulob din Manchester City na Ingila da kuma FC Barcelona da ke Sifen a gasar gasar zakarun kulob-kulob na Turai watau UEFA Champions League da aka yi a ranar Talatar da ta wuce a filin wasa na City. FC Barcelona ce ta lallasa ta City da ci 2-0.
Sai dai kocin City Manuel Pellegrini ya nuna shakkunsa kan yadda alkalin wasan ya bayar da bugun fanariti a daidai minti na 54 bayan da dan kwallon City Martin Demichelis ya kayar da Lionel Messi gab da tsallake layin shiga ragar City amma duk da haka alkalin wasan ya ba dan kwallonsa jan kati tare da bugun fanariti.
Kocin ya ce alkalin wasan bai nuna adalci wajen bayar da jan kati tare da ba FC Barcelona bugun fanariti ba. Ya ce kamata ya yi ya bayar da bugun tazara ne tun da al’amarin ya faru ne a wajen gidan City kuma Lionel Messi ya yi tsallen badake ne don haka bai cancanci a bashi bugun fanariti ba.
“Tun farko bai dace a ce alkalin wasan da ya fito daga Swidin ne zai hura wasa mai zafi irin wannan ba, don shi ne alkalin wasan da ya taba hura wasannin da Barcelona ta yi a baya kuma yanzu yana neman ya saka musu ne a bisa kuskuren da ya tafka musu a baya na kin ba su bugun fanariti don haka na yi mamakin yadda aka ba shi damar hura wasanmu a wannan karo”, inji Pellegrini.
Sai dai akwai yiwuwar Hukumar kula da shirya gasar watau UEFA ta hukunta kocin a kan wadannan kalamai da ya yi.
Tsallen badake Lionel Messi ya yi wajen samun fanariti -Kocin City Pellegrini
Kocin Manchester City Manuel Pellegrini ya nuna bacin ransa a kan yadda alkalin wasa Jonas Eriksson dan asalin Swidin (Sweden) ya hura wasa a tsakanin…