✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Tsakanin Tinubu da Osinbajo za a kara a zaben dan takarar APC —Kabiru Gaya

Amaechi da Fayemi da Umahi sun janye wa a wadanda suke goyon baya

Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Kabiru Ibrahim Gaya, ya ce jam’iyyar APC ta sake rage yawan mutanen da za su fafata a zaben dan takarar shugaban kasarta zuwa biyu daya yankin Kudu.

Kabiru Gaya, wanda shi ne Sanata mai wakiltar Kano ta Kudu a Majalisar Dattawa ya ce mutum biyun da za su fafata su ne Uban Jam’iyyar na Kasa, Bola Tinubu da kum Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo.

Ya bayyana haka ne hrar da tashar talabijin ta Channels ta yi da shi kai-tsaye daga zauren taron da ke gudana a Danlin Eagles Square da ke Abuja.

Amma a nasa bangaren, Darakta Janar na Kwamitin Yakin Neman Zaben Osinba, ya ce sauran mutum uku da ke zawarcin tikitin daga yankin, sun janye ne wa wadanda suke goyon baya.

Mutum ukun da suka janye din, a cewarsa, su ne Gwamnan Jihar Ekiti, Kayode Fayemi; tsohon Mninistan Sufuri, Chubuike Rotimi Amaechi da kuma Gwamnan Dave Umahi na Jihar Ebonyi.