✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsadar rayuwa: Nama ya gagara, an koma cin awara

Wata mai sana’ar sayar da awara a Abuja, Hannaru Musa, ta ce mutane da dama sun daina sayen nama ko kifi, sun dawo cin awara…

Wata mai sana’ar sayar da awara a Abuja, Hannaru Musa, ta ce mutane da dama sun daina sayen nama ko kifi, sun dawo cin awara saboda tsadar rayuwa.

Hannatu, wadda ke sana’ar awara a yankin Bwari, ta bayyana cewar tsadar da nama da kifi suka yi ta sa mutane sun hakura da su, inda suka koma sanya awara a cikin abinci.

Hannatu wadda ta bayyana cewa awara na dauke da sinadarin protein mai yawan gaske, ta ce “akwai wani kwastomana da ya gaya min cewa duk iyalansa yake saya wa awara su sa a abinci.

“A tunanina, yadda awarar take yanayi da nama ya sa shi yin hakan. Za ka iya sanya awara a cikin miya, romo ko ma abinci.”

Wata mai sayen awara, Madam Christine Douglas, ta ce ba ta taba cin awara ba sai da ta zo Abuja kimanin shekaru biyar da suka gabata.

Ta bayyana cewa wata makwabciyarta ’yar Arewa ce ta fara ba ta, kuma tun daga lokacin ta rungumii cin ta, inda take zuwa ta bi layi ta saya.

“Akwai dadi, kuma ni ma na koya wa wasu mata cin ta.

“Ina son yadda ake kawata ta da kayan hadi; ga ta da dadi idan aka hada da shinkafa.

“Yanzu da rayuwa ta yi tsada kuma ina amfani da ita domin samun cikakkun sinadaran kara lafiya a abinci,” inji shi.

Wata masaniyar abinci mai gina jiki, Dokta Kemi Adegoke-Abraham, ta ce awara na dauke da sinadaran Bitamin mai yawa da kuma carbohydrate mara yawa.

Don haka abu ne mai kyau marasa bukatar abinci mai nauyi su rika cin ta.

“Yana da kayau masu cutar suga su rika cin ta kuma taba rage hadarin kamuwa da cutar kansar mama,” inji ta.

(NAN)