Kungiyar Likitoci ta Najeriya (NMA) ta nemi Gwamnatin Tarayya ta sassauta kudin jarrabawar likitoci masu neman kwarewa saboda yadda lamarin ya zama babban kalubale ga likitocin.
Shugaban kungiyar NMA reshen Jihar Kano, Dokta Isyaku Usman, ya bayyana tsadar kudin jarrabawar ta sanya likitocin suna barin Najeriya zuwa wasu kasashe domin neman sauki.
“Muna kira ga Gwamnatin Tarayya da ta soke kudin jarrabawa da aka sanya a wadannan ’yan kwanaki a kan likitoci masu neman kwarewa a fannoni daban-daban.
“Domin a yanzu hakan ya janyo likitoci suna barin gida zuwa kasashen waje, duk da yake cewar akwai wasu dalilan, to amma wannan yana kan gaba.”
Ya yi wannan kira a wani bangare na taron shekara-shekara da kungiyar ta fara gudanarwa a ranar Litinin.
Dokta Isyaku ya yi kira ga Gwamnatin Jihar Kano da ta sakar wa likitocinta tallafin da take ba su don biyan kudin jarrabawar da za su yi ta neman kwarewar, duba da cewa a yanzu haka tuni aka fitar da takardu a kan hakan.
Da yake karin haske game da taron na shekara-shekara, ya bayyana cewa a karshen taron za a samar da sabbin shugabannin kungiyar wadanda za su ja ragamarta a nan gaba.