✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsadar fetur ta sa Buhari komawa motoci masu aiki da gas

Minista a Ma'aikatar Man Fetur ya ce ana motocin gwamnati na komawa kan iskar gas

Minista a Ma’aikatar Man Fetur, Timiprey Sylva, ya ce tsadar fetur ta sa ana mayar da motocin Shugaban Kasa da ministoci masu aiki da gas.

Sylva ya ce tuni motocin ofishinsa suka koma aiki da gas kuma motocin takwarorinsa ministoci da ‘yan Majalisar Dokoki ta Kasa na kan sahu.

“Mun kammala tattaunawa da ministoci kan mai da motocinsu masu amfani da gas.

“Su ma Majalisar Dattawa da Majalisar Wakilai, za mu tattauna batun mai da nasu motocin masu aiki da gas domin ya fi sauki sosai”, inji Sylva.

Lokaci ya yi

Ministan ya ce lokaci ya yi na daina dogaro da fetur a matsayin makamashi saboda tsadarsa.

Hakan a cewarsa ita mafita kuma nan da ranar 30 ga Nuwamba, 2020 za a kaddamar da shirin a kasa baki daya.

Sai dai ya koka cewa duk da Najeriya na sahun farko na kasashe masu arzikin gas a Afrika, har yanzu an fi amfani da shi ne a birane da manyan garuruwa.

“Kuma an shaida min a yanzu haka kamfanin Dangote na samun saukin kashe kudaden shan mai da kashi 50 cikin 100. Wato a yanzu rabin abin da ake kashe wa motocin na fetur ne ke isa a sayi gas”, inji shi, da yake cewa kamfanin ya koma amfani tireloli masu aiki da gas.

Wannan bayani ya zo ne daidai lokacin da farashin fetur ya tashi daga Naira 161 ya koma Naira 170.

Yan Najeriya na ta sukar karin farashin fetur dadda ke zuwa a daidai karshen shekara.