Cibiyar Koyar da Fasahar Sufuri ta Najeriya (NITT), ta ce za ta fara canza wa jama’a motoci masu amfani da man fetur su koma amfani da Gas, sakamakon tsadar fetur din.
Shugaban cibiyar, Dokta Bayero Salih-Farah, ne ya bayyana hakan lokacin da yake jawabi ga manema labarai a hedkwatar cibiyar da ke Zariya, a Jihar Kaduna.
- Gwamnan Bauchi ya jagoranci Sallar rokon ruwa
- Har yanzu Najeriya ta fi kowacce kasa arhar man fetur a nahiyar Afirka – IPMAN
Ya ce cibiyar za ta fara gudanar da aikin ne a ofisoshinta da ke dukkan shiyyoyin siyasa guda shida da ke kasar nan.
Dokta Bayero ya kuma kara da cewa, makarantar ta fara wannan gagarumin shiri tun kimanin shekarar da ta gabata, kuma za ta shirya tarukan horaswa a sassan kasar nan a makonni uku masu zuwa domin fara aiwatar da aikin gadan-gadan.
Kazalika ya ce Gas nada matukar sauki fiye da fetur a halin yanzu, wanda ’yan Nigeria za su samu sauki wajen kashe kudade da zaran sun sauya ababen hawan nasu daga amfani da fetur zuwa gas.
Daga nan sai ya yi kira ga ’yan Najeriya su dauki wannan dama wurin bayar da hadin kai don samun nasarar shirin.